Jima'i

Amfanin Fitar Da Maniyi A Kullum Ga Maza Ma’aurata


Maniyi yana da matukar mahimmanci a jikin namiji. Domin sai dashi namiji zai iya haihuwa.


Ruwan maniyi wani ruwane mai kama da madara yana da kauri da yauki da yake adane a marainan duk wani namiji. Maza suna fitar da maniyi zuwa mahaifar mace ne a lokacin da suka yi zuwan kai a yayin Jima’i.


Yadda tara maniyi a jikin duk wani namiji yake da amfani, haka ma fitar da shi ga duk wani namiji yake da alfanu.


Ga mazan da basu da damar fidda shi, a kullum suna cikin kullewa da ciwon mara mussamman idan yayi yawa a tare dasu. A duk lokacin da sha’awar su ya motsa kuma basu damar tsirtar da shi ba. Tofa zasu gamu da ciwon mara mai tsanani.


Masana sun bada shawaran cewa, yana da kyau a duk rana duk namiji ya samu damar zubda maniyi a kalla sau daya. Hakan a cewar su, yana karawa namiji lafiya da kuma maniyi mai inganci da zai iya samar da haihuwa. Sannan yana kawar da hatsarin kamuwa da ciwon daji na mafitsara ga maza.


Sai dai kuma mazan da suka manyanta ba zasu samu damar fitar da maniyinsu ba kamar yadda maza masu karancin shekaru zasu iya ba.


Sai dai kuma mazan da suke da ciwon shuga suna iya samun sauki sosai da karin lafiya idan zasu samu damar fitar da maniyi akai-akai.


Yana da kyau maza su fahimci cewa, tara maniyi a jikin namiji ba tare da fitar dashi ba hadari ne ga maza. Yawan fitar dashi waraka ne ga maza. Da fatan maza ma’aurata zasu kokarta wajen cin matansu a kullum domin fidda maniyi akokarin samun lafiya.

See also  Dalilan Da Suke Hana Wasu Matan Sha'awar Jima'i

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button