Tarihi

Tarihin Docta Ishola Oyenusi Dan fashi Da Makami Mafi Hadari A Tarihin NajeriyaIshola Oyenusi, wanda aka fi sani da Doctor Oyenusi, ya kasance dan fashi da makami da ya addabi al’ummar Legas da sauran garuruwan da ke makwabtaka da ita a shekarun 1970.

Ishola Oyenusi da ’yan kungiyarsa guda shida sun kware wajen sace motoci, fashin bankuna, masana’antu, shaguna da kashe mutane kamar kaji.


Shin da gaske Ishola Oyenusi Likita ne?


Dokta Oyenusi, kamar yadda ake kiransa, ba likita ba ne a sana’a, amma ya ɗauki lakabin don jin daɗin Kansa.

Ya bayyana cewa iyayensa ba su da ikon Taimaka Masa Wajen Ci gaba da karatunsa na Sakandare wanda hakan ne ya tilasta masa shiga Sana’ar fashi. Don haka ba tare da karatun sakandare ba, Oyenusi ko ta yaya ba zai Taba zama likita ba.


Fashin Da Oyenusi Ya Fara Yi


Oyenusi ya fara sana’ar sata ne ta hanyar kwace mota (wacce mai ita ya mutu a Fashin) saboda kawai budurwar sa tana bukatar kudi. Wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa Oyenusi Dan soyayya ne.

Ya sayar da motar a kan kudi Naira 400 ya ba budurwar tasa kudin. An kuma ce Oyenusi yana da zafin rai da Taurin kai. A lokacin da aka kama shi, sai ya Dakawa wani dan sanda da ke Kusa da shi Tsawa Ya ce, “Mutane irin ku ba sa magana da ni haka, sa’ad da nake da makami, ina harbe su!”

Sunan Dokta Ishola Oyenusi ya fara fitowa fili ne bayan yakin basasar Najeriya ya kawo karshe a shekarar 1970. Ya yi wa bankuna da jama’a fashi dare da rana, kuma baya barin wani daga cikin wadanda yayiwa Fashin ya rayu, yana kashe su duka! Wannan ya sa aka masa suna “Doctor fashi da kisa”. (Doctor rob and kill“.)

A lokacin Zamanin sa mai ban tsoro, Ishola Oyenusi ya yi alfahari cewa “harsashi ba zai iya kashe shi ba”. Wataƙila ya manta cewa wanda yake rayuwa da takobi tabbas zai mutu da takobi. (Makashin Maza Shi maza Kan Karshi).

Oyenusi ya yi kaurin suna har wasu na kallonsa a matsayin “wanda ya Fara zama Rikakken dan fashi da makami a Najeriya”, bayansa kuma akwai Lawrence Anini, Babatunde Folorunsho (Baba oni lace), Shina Rambo, Buraimo Jimoh da sauransu.
See also  Takobin Allah: Tarihin Khalid Ibn Al-Walid Kashi Na Farko


Kamun Ishola Oyenusi


Sai dai kuma babu wani abu da zai dawwama, kuma kamar yadda karin maganar Yarabawa ke cewa, yau da kullum na barawo ne yayin da rana ta mai gida ce.

A ranar 27 ga Maris, 1971, ‘yan sanda sun kama Oyenusi a wani samame da suka kai, A yayin Wani fashi da makami, in da shi da gungun ‘yan kungiyarsa suka kashe wani dan sanda mai suna Mista Nwi tare da sace dala 28,000 a lokacin.

Kunya ta Kama Dokta Ishola Oyenusi yayin da aka gurfanar da shi a gaban Shari’a kuma aka same shi da laifi sannan aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar bindige shi.

Oyenusi ya furta cewa ba zai mutu shi kadai ba saboda bai aikata laifin shi kadai ba.

Ya amayar da sunayen sauran mambobin kungiyar da suka hada da: Joseph Osamedike, Ambrose Nwokobia, Joel Amamieye, Philip Ogbolumain, Ademola Adegbitan da Stephen Ndubuokwu.

A wancan lokaci ana aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama’a, don haka lokacin da aka kai Oyenusi zuwa Bakin Teku na Bar Beach da ke Legas inda za a kashe shi, ‘yan Najeriya sama da 30,000 ne suka yi ta murna da annashuwa suna jiran ganin mutumin da ya yi musu ta’addanci harsasai masu zafi sun Gama dashi.

An ce wasu ma’aikatan gwamnati ma sun kawo akwatin gawa a wurin da za a harbe shi, su na yi masa ba’ar cewa ga babban dan fashin nan wanda a yanzu ba wani abu ba ne illa Dan Akuyar da numfashin ta zai kare a kowane lokaci.

Motoci dauke da Oyenusi da Yan kungiyarsa da masu zartar da hukuncin sun isa wurin da za a Kaddamar da hukuncin ne da misalin karfe 10:00 na safe.

Jama’a sun yi ta yi masu ba’a, musamman Oyenusi wanda da gaske suke yi domin ganin ya mutu. Oyenusi ya sa doguwar riga mai duhu kuma An daure hannunsa a bayansa.

Mintuna kadan kafin a harbe shi, Oyenusi ya shaida wa manema labarai cewa da iyayensa sun tura shi makarantar sakandare da Bai Shiga Fashi Da Makami Ba.

Ya kuma ce, “zan mutuwa saboda laifin da na aikata”. An daure Oyenusi da sauran masu laifi a gungumen a jikin Dirka.

Sojojin sun yi layi a gabansu da bindigogi. Wasu daga cikin masu laifin sun yi kukansu na karshe a Gaban kyamarori. Can Sai wata babbar murya ta fitar da kalmar “wuta”! An yi wa Oyenusi da sauran miyagu Ruwan harsasai a jikinsu.

Wannan shine Abin bakin cikin da Ishola Oyenusi ya rayu da harsashi ya mutu da harsashi. Hukuncin kisa da aka yi wa Dakta Ishola Oyenusi ya sa titunan Legas suka zama ba kowa cikin dare. Iyalai sun kulle kansu a Cikin gida saboda tsoron kada wasu yaran Oyenusi suyi musu Ramuwar Gayya.

Sunan Ishola Oyenusi zai kasance har abada a cikin tarihin aikata laifuka a Najeriya.

See also  Tarihin Hudhayfa ibn al-Yaman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button