Tech

Yadda zaka dawo da hotunan da aka rasa a cikin waya

Sau da yawa wasu suna adana hotuna ne domin tarihi, wasu kuma a garesu ba haka bane, wasu suna daukar hotuna su adanasu ne domin hujja ta wani abun, ko kuma shaida ta faruwar wani abun wanda akayi kuma suke tananin za’a iya neman shaida akan faruwar abun, duba da yanayin da rayuwa ta kaimu a halin yanzu na rashin gaskiya da ƙarancin riƙon amana.

A taƙaice dai adana hotuna yana da matuƙar muhimmanci, haka zalika kowa zaiso yaga ya maido da hotunan daya rasa madamar suna da muhimmanci a wajenshi, imma shine ya gogesu da kanshi imma dai wani ne ya goge mashi su.

Kamar yadda muka sani cewa a computer wato na’ura mai ƙwaƙwalwa akwai wani waje da yake ajiye duk wani abun da aka goge daga cikin computer ‘din har sai anje an goge abun daga can baki ‘daya kafin ya fita duka, wato kamar kwandan shara zamu ce ma wajen, abun yana kasancewa ne kamar yadda muke rayuwarmu ta gida, duk abubuwan da bamaso idan muka tattarasu muna zubasu ne a kwandan shara kafin daga nan mu kwashe su zuwa bola mu zubar, to kafin mukai su bola idan muka tuna mun saka wani abu mai muhimmanci aciki zamu iya dubawa mu ‘dauki abunmu kafin ace mun kaisu bola baki ‘daya.

Itama waya tana da makamancin irin wannan tsarin sai dai nata yasha banban da irin wanda nayi bayani, wato na computer.

Shi wannan wanda zanyi bayani akanshi, wata folder ce mai suna “Thumbnails” ita a 6oye take sai idan an bude wani waje kafin take bayyana.

See also  Best 5 Steps To Improve Your Programming Skills

Amfanin ita wannan folder shine duk wani hoto wanda ya shigo cikin wayarka madamar kayi amfani dashi zata dauki hotonshi ta adana acikin folder ‘din, sai dai kawai bai kai quality ‘din ainihin hoton ba.

Ba iya hoto kadai take dauka ta adana ba, harma video idan ka kalla tana daukar video din hoto kamar irin screenshot ta adana duka acikinta.

Idan da zaka amshi wayar wani ka bude folder ‘din ka shiga bude hotunan dake cikinta lallai zaka ga dukkan wani hoto ko video wanda ya ta6a shigowa cikin wayar madamar ba’a biyo har ciki aka gogeshi ba.

Matakan da zaka bi wajen dawo da hotunan da aka rasa acikin waya sune…

Da farko zaka shiga cikin file manager ‘din wayarka wato inda ake ganin kan waya (internal memory) da kuma cikin memory card (external memory) idan ka shiga zaka shiga cikin internal memory ‘dinne wato kan wayar, sai ka nemi wani waje mai alamar ido ️ daga ƙasa kamar yadda ka gani a hoton dana saka, amma a wasu wayoyin yake haka a wasu kuma kawai an rubuta ne.

Mataki na biyu bayan ka shiga wajen zaka samu ne yana akan “Hide Files” sai ka mayar dashi akan na saman wato “Show Hidden Files” ma’ana ka bude fayilolin da suke a rufe ba’a ganinsu kenan kamar yadda na gaya maku cewa ita folder ‘din nan ta “Thumbnails” a rufe take sai an budeta ake ganinta.

Mataki na uku shine da zaran ka tabbata ka bude fayilolin da suke a rufe sai ka fara duba folder ‘din da kayi abun dominta wato “Thumbnails” a wasu wayoyin zaka ganta ne a fili ba’a cikin wata folder ba, a wasu wayoyin kuma zaka ganta ne a cikin wata folder mai suna DCIM.

See also  YADDA ZAKU IYA DAWOWA DA DUK WANI MESSAGE NA WAYARKU DAYA GOGE

Matakin gaba bayan ka nemo folder ‘din sai ka shiga cikinta kai tsaye anan ne zaka fara ganin hotuna kala-kala harda ma wa’danda baka san dasu ba.

Abunda zakayi anan shine sai kayi mark ‘din hotunan dukansu kayi move (matsarwa) ko kuma kayi copy (kwafa) sai ka fitar dasu daga cikin folder ‘din ka kaisu can cikin wata folder ‘din wadda ita bata 6oyewa ka adanasu acan.

Wannan shine iya abunda zakayi ka dawo da hotunan da aka rasa acikin waya, kuma ba’a kaisu ajiya wani waje ba can daban.

Masha Allah.
Koyon wannan abun yana da muhimmanci sosai ga al’umma musamman ma masu binciken miyagun mutane ko kuma jami’an tsaro saboda sau tari za kaga an kama mai laifi an amshi wayarshi anason aga wani ko wata shaida ta wani abu amma sai kaga an rasa ganin komai saboda ya gogesu daga wayarshi, kuma ba lallai yasan ana iya ganinsu ba tanan.

Allah yasa mu dace, Amin.

✍ Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button