Tarihi

Tarihin Hudhayfa ibn al-Yaman

Ḥuzaifa ibn al-Yamān ( Da Larabci: حُذَیفة بن الیمان ) sanannen sahabban Manzon Allah (SAW) ne kuma daya daga cikin mutanen farko da suka musulunta. Ya kasance tare da Manzon Allah (SAW) a yakoki da dama a farkon shekarun Musulunci. Ya kasance na musamman kuma makusancin Imam Ali (AS). A wasu hadisai an ambace shi a matsayin daya daga cikin manyan sahabbai hudu na Imam Ali (AS).

Ya ruwaito hadisai dangane falalar Imam Ali (AS) da Ahlul Baiti Ya kuma halarci Yakukkuwan halifofin farko, ciki har da yakin Nahawand.

Abu Abd Allah Hudaifa ibn al-Yaman ibn Hisl ko Husayl dan kabilar Abs ne a kasar Yemen. Al-Yaman Mahafinsa ya tafi madina kafin bayyanar musulunci kuma Zauna a gidan Abdul-Ashhal daga gidan Aws, ya auri Rubab diyar Ka’b. Ya haifi ‘ya’ya uku maza daga Rubab: Sa’ad, Safwan, da Mudlaj da ‘ya’ya mata uku Layla, Salama, da Fatima.

Huzaifa A Zamanin Manzon Allah (SAWW)

Huzaifa yana daya daga cikin mutanen farko da suka musulunta musulunta. Ya yi hijira zuwa Madina bayan Annabi (SAW). Yana daga cikin Muhajirun, a daya bangaren kuma, tun da ya yi tarayya da wani dangi a Madina, shi ma an dauke shi a matsayin daya daga cikin Ansaru. Annabi (SAW) ya bai wa Huzaifa zabin ko ya kasance cikin Muhajirun Ko Ansar kuma ya zabi ya zama daya daga cikin Ansar. Annabi (SAW) ya tabbatar da zabinsa kuma ya kulla Yan’Uwantaka tsakaninsa da Ammar, daga Muhajirun.

Huzaifa bai halarci yakin Badar ba, amma ya halarci yakin Uhudu tare da mahaifinsa. Musulmi sun ka*she mahaifinsa bisa Kuskure

See also  Tarihin Docta Ishola Oyenusi Dan fashi Da Makami Mafi Hadari A Tarihin Najeriya

A Ya*kin Khandaq Manzon Allah (SAW) ya nemi Huzaifa da yaje ya samo bayanai kan sansanin makiya, kuma ya yi nasarar yin hakan. Ya kuma halarci wasu Yakukuwan Manzon Allah (SAWW)

Manzon Allah (SAWW) ya aminta da shi. Annabi (SAW) ya sanar da shi abubuwa da dama da zasu faru a gaba na fitina, da haqiqanin halayen wasu mutane da munafukai. Musamman lokacin da Annabi (SAW) yake dawowa daga Tabuka ya gaya wa Huzaifa sunayen dukkan munafukai. Wannan shine dalilin da ya sa mawallafan tarihin rayuwarsa suka kira shi “Sahib al-Sirr”.

Annabi (SAW) ya ce da Huzaifa da Imam Ali (AS) cewa “sun fi kowa sanin munafukai fiye da sauran mutane”.

Huzaifa ya ruwaito hadisai dayawa. An san shi da takawa, Mara son zuciya, da gujewa tara dukiya.

Huzaifa A Lokacin Halifofi

Sayyadina Umar Ibn Al-Khattab (RA) ya nada Huzaifa a matsayin kwamandan yakin Nahawand. Ya jagoranci kwamandan sojoji ya ci Nahawand. Sannan ya ci sauran garuruwan Iran. An kuma nada shi a matsayin shugaban Al-Mada’in (Wani Gari Ne a Iraki) a zamanin Sayyadina Umar Ibn Khattab (RA)

A zamanin Sayyadina Usman (RA) Huzaifa ya halarci jana’izar Abu Zar. Ya kuma bai wa sayyadina Usman (RA) bayanai dalla-dalla na Kur’ani daban-daban, ya kuma ba da shawarar cewa a hada juzu’i na Alkur’ani guda daya.

Huzaifa a zamanin Imam Ali (AS)

Ana yi masa kallon daya daga cikin manyan sahabban Imam Ali (AS) guda hudu. Al-Kashshi ya kawo hadisin da ake ganin Huzaifa a cikin mutane bakwai Wadanda Allah ya yi ni’ima da falalarsa ga mutane. Wadannan mutane bakwai sun halarci jana’izar Fatima al-Zahra (AS) .

See also  Cikakken Tarihin Facebook

A lokacin da Imam Ali (AS) ya isa yankin Dhi Qar a hanyarsa ta zuwa yakin Jamal Huzaifa ya gaya wa sahabbansa cewa: “Ku raka Amirul Mu’minin (AS) kuma magajin Manzon Allah (SAWW) A taimaka masa”. Ya ruwaito hadisai dangane da falalar Imam Ali (AS) da Ahlul Baiti (AS).

Al-Mas’udi ya ruwaito cewa ‘ya’yan Huzaifa guda biyu Safwan da Sa’ad sun raka Imam Ali (AS) a yakin Siffin kuma a can ne suka yi shahada. Amma a cewar al-Tabari, Sa’ad yana raye a lokacin tashin Tawwabun : Sulayman ibn. Surad ya nemi taimakonsa ya taimaka Masa.

Mutuwa

Huzaifa ya rasu a shekara ta 36 /656-7 [37] ko 37 / 657-8 a cikin Birnin Al-Mada’in (Iraƙi) Jikokin Huzaifa suna cikin Al-Mada’in har zuwa karni na 3/9.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button