Jima'i

Abunda Yasa Wasu Matan Suke Da Jarabar Tsiya Idan Suna Gaf Da Ganin Wata


Mata sukan samu sauyin yanayi a duk lokacin da suka kusa soma yin al’ada. Wanda yawan sha’awa yana daya daga cikin abubuwan da wasu matan suke fiskanta. To meke jawowa matan wannan sha’awar?


Yayi da mace ta kusa soma al’ada jinin dake gudana a jikinta yana kara yawa da guda musamman na wajen Al’uranta, wanda hakan yaka jawowa mace sha’awa.
Haka nan sinadaren dake jikin mace suna sauyawa, wanda cikin sauyin nasu da akwai yawan sha’awa.


progesterone sinadari ne a jikin mace dake sata jin sha’awa, idan mace ta kusa soma ganin wata wannan sinadarin yana kara yawa a jikin mace wanda hakan na jawo mata sha’awa.


Haka nan yanayin samun kwanciyar hankalin mace shima yana kara mata sha’awa gaf da soma al’ada.


Sai dai kuma babban hikimar da Allah SWT Ya sa mata suke jin sha’awa a wannan lokacin shine. Ganin a wannan yanayin mace na iya samun ciki idan namiji ya kusanceta, don haka sai Allah Ya kaddara mata sha’awa domin ta bukaci yin Jima’i da mijinta a wannan lokacin ko za a samu dacewa.


Akwai matan da basu da sha’awa sam, sai a irin wannan yanayin kadai suke yi. Don haka Allah sai ya cusawa mata wannan lamarin domin ayi dace da shigan ciki.
Bama mutane kadai suke samun kansu a hakan ba. Hatta dabbobi suma sha’awar su na karuwa a irin wannan lokacin.


Lokuta guda uku ne mata suke samun kansu da sha’awar Jima’i. Kamin soma al’ada, lokacin da suke al’ada da kuma kwanaki 3 na bayan kammala al’adar.


Kada kiji wani kunya ko tsoro idan kina cikin matan da suke da wannan halittar. Domin haka nan Allah Ya tsara kuma ba rashin lafiya bane.

See also  Hadarin Yin Wasa Da Matarka A Lokacin Al'ada

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button