YADDA ZAKU IYA DAWOWA DA DUK WANI MESSAGE NA WAYARKU DAYA GOGE
Yana da amfani matuƙa yau ace ka iya dawowa da duk wani saƙon SMS na waya wanda aka ta6a gogewa imma da ganganci ne imma a cikin rashin sani ne. Iya yin hakan na iya taimakonka a rayuwa ko kuma ya baka dama ka taimaka ma wani a rayuwa. Akwai ƙaddarori kala-kala da suke hawan bayin Allah wanda mutum zai iya kasancewa baya da wata shaida sai wani saƙo da aka ta6a turo mashi, kuma gashi saƙon ya goge, Allah ya kyauta. Bayan nan akwai bincike-bincike da suke kamawa akan wani ko wata har za’a samu damar amsar wayarsu dan duba wani saƙo amma sai a samu sun goge saƙon, to duk za’a iya amfani da wanan hanyar domin samun damar ganin saƙon da aka ta6a gogewa a wayarsu.
Haka zalika kamar yadda yanzu rayuwa tayi wuya, kowa na saka ido akan wanda kulawarshi take a ƙarƙashinsa domin lura da tarbiyarshi ta 6angaren irin mutanen da yake mu’amula dasu a 6oye, za’a iya amfani da wannan hanyar a dawo da duk wani saƙo daya ta6a shiga wayarshi a matsayin SMS kuma a turashi inda akeso dan yin bincike sannan a goge app din da history na turawar ba tare da mai wayar ya sani ba, madamar wayar tazo hannun wanda keson yin binciken.
1- Da farko za’a shiga cikin playstore ayi download na app mai suna: E2PDF, sai ayi install nashi a saman wayar da ake neman saƙon da aka goge su dawo, bayan app din ya bude zai bada bayanai da buƙatar amincewa, sai a danna agree tare da proceed kamar yadda aka gani a hoto na farko.
2- A mataki na 2 sai a danna inda aka rubuta click to continue.
3- Za6i guda 2 zasu bayyana sai a danna na farkon wanda yake a sama na SMS kenan.
4- Anan kuma zai bada damar a saka ma file din suna yadda ake da buƙata, daga nan sai a danna wajen da aka rubuta create sms backup.
5- Daga nan app din zai nemi izinin samun access da wayarka ta yadda zai binciko duk wani saƙo da aka ta6a turowa ta sigar SMS, sai a danna Allow.
6- Yana kammalawa zai nuna maka save file, sai a danna wajen save file din.
7- Anan ne kuma zai bada damar a tura file din zuwa wani waje idan ana buƙata, idan kuma bude file din ake so ayi sai a danna wajen WPS dan samun karanta saƙonnin ta cikin PDF.
8- Bayan saƙonnin sun bude a page-page, daga can ƙasa a hannun dama za’aga adadin yawan saƙonnin, sannan idan aka danna gefen damar za’a ga page na gaba ya bayyana.
Allah ya taimaka.
© Abu Ibrahim