Tech

Manyan Dalilan da Suke Sanya Dalibai Faduwa Jarrabawa tareda Bayani Akan Yadda Zaka Guje Musu

Dalibai da Dama Sukan Fadi Jarrabawar Karshe ta Kammala Makaranta ko kuma Aji, Alhalin Sunci Jarrabawarsu ta Zangon Farko da na Biyu, ko kuma Sunci Dukkannin Jarrabawoyin da suka Gudanar a Makarantar ma Baki Daya,





•Shin Meyake Jawo Hakan ?



> Kokarine Basudashi ?



Ko kuwa



• A ina Matsalar take ?


> Hakika Ƙoƙarin Mafi yawan Ɗalibai Yakan ragu, haka Zalika Irin Nasarar da suke Samu a Jarrabawoyinsu ma Sukan Ja Baya, Dazarar Aski Yazo Gaban Goshi, Ma’ana Idan Suka Bude Ido suka Gansu a Babban Aji Wanda Dagashi Zasu Kammala Makaranta, ko kuma Idan suka tsinci Kansu a Zangon Karatu na Karshe Wanne dagashi Zasu Kammala Ajin da suke su tsallaka Aji na gaba, Wanda Wannan Shine Babban Dalilin da Kansa Daliban Faduwa Jarrabawoyinsu,





•Mafita Anan Itace Yanada Kyau Dalibai su dinga Mayar da Kai Akan Karatunsu, kuma Su Guji Daina Bibiyar Littattafansu tareda Kama Sharholiya Da Zarar sun kusa Kammala Karatunsu, Wanda wannan Itace Dabi’ar Mafiyawan Daliban Wannan Zamani,


> Dalili Na Biyu Dakansa Irin Wadannan Dalibai Faduwa Jarrabawoyinsu kuwa Shine Fitowar Abinda Ba’a koya musu ba a cikin Jarrabawar : Tabbas hakan tana faruwa, Domin kuwa Jarrabawar Karshe Jarrabawace da takan hado Dukkannin darussan da aka koyawa Dalibi a Daukacin Aji ko Makarantar da Yake Gab da Kammalawa, Wanda hakan Yakan Bada Damar Ayi Masa Tambayoyi daga Cikin Dukkannin Darussan da Aka Koya masa a Wannan Ajin ko Makarantar Baki Daya, Wanda Idan Dalibai basuyi Sa’a ba har Darussan da Ba’a koya musu bama Sukan Iya Fitowa a Takardar Jarrabawar tasu, Tunda Mafi Yawan Hukumomin Shirya Jarrabawa tareda Malamai suna yin Amfani da Teaching Syllabus ne Wajen Tsara Tambayoyinsu ga Dalibai,





• Mafita Anan Itace Yanada Kyau Dalibai su dinga Bibiyar Darussan da Aka Tsara Koya Musu tareda Bincike Akai ta hanyar littattafai da Yanar Gizo, Dukkannin Darasin da Suka Gani a Syllabus suyi Kokarin Bincike Akansa Domin su Fahimceshi koda kuwa Ba’a Koyar dasu Darasin a Aji ba, Saboda Su Hukumomin Shirya Jarrabawa bazasu San Ba’a koya maka Shiba, Saboda haka Zai iya fitowa a Jarrabawa, A Bangaren Malamai kuwa Yanada Kyau suma su kasance Masu Kokarin Cika Alkawurran da Suka Dauka, ta hanyar koyar da Daliban su Dukkannin Darussan da Hukumar Ilimi ta Bada Umarnin a Koyar dasu, Hakanne Zai kawo Karshen Wannan Matsala.

See also  Yadda Zaka Ɓoye Number Ka Yayin Tura Saƙo (Text Message)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button