SHIN ZAI YIWU A IYA FASSARA KO KUMA KOYAR DA LITTAFAN KIMIYYA DA HARSHEN HAUSA ?
SHIN ZAI YIWU A IYA FASSARA KO KUMA KOYAR DA LITTAFAN KIMIYYA DA HARSHEN HAUSA ?
Daga:
Baban mu Professor Malumfashi Ibrahim
Duk da cewa ba lokaci da za a tsaya a ce wani abu mai faɗi game da wannan batu, amma zan ɗan ɗofana baki kaɗan.
Ita karantarwa, musamman ta Kimiyya abu ce da ke buƙatar lokaci da dagewa da naci da kuma goyon baya daga dukkan waɗanda abin ya shafa, musamman hukuma da mu waɗanda ake son yi wa aikin.
Ba abin da bai yiwuwa idan an mayar da hankali.
Abubuwa guda biyu zan ba da misali da su, na farko shi ne a lokacin da UNESCO ta zaɓi Hausa a matsayin ɗaya daga cikin harsunan da za a rubuta Tarihin Afirka a shekarun 1980 mutane da yawa sun ɗauka aikin ba zai yiwu ba, amma da aka tattara masana aka samu shekara biyu ana yi, yanzu ana da littafin Tarihin Afirka Kammalalle cikin Hausa, wanda duniya ke tinƙaho da shi.
A shekarun 1990 kuma Farfesa Hambali Jinju ya fitar da littafinsa GARKUWAR HAUSA DA TAFARKIN CIGABA inda ya samar da jagora na koyar da kimiyya cikin Hausa, dubban kalmomin Kemistiri da Fisik da Bayoloji duk an fassara su, kuma littafin ya tabbatar da cewa idan ana son koyar da kimiyya cikin Hausa za a iya.
A halin da muke ciki ba wani ɓangare na ilimin kimiyya da ba a ƙoƙarta sarrafa shi da Hausa ba. Ba tun yau ake wannan ƙoƙari ba, domin tun a shekarar 1957 Abubakar Imam da East sun wallafa littafin Ikon Allah (1-5) wanda ya yi bayanin halittu iri-iri.cikin Hausa, wanda za a iya cewa shi ne littafin farko da aka fara koyar da Geography da shi cikin Hausa.
A halin yanzu ina iya sanar da masu buƙata ba wani fanni na kimiyya da ba a taɓa fassara ko dai dukansa ba ko wani ɓangare domin koyarwa da Hausa. Matsalar a kullum ita ce ɗaukar- sakainar-kashi da ake yi wa fannin.
- An fassara dukkan littattafan kimiyya na Firamare.
- An fassara dukkan littattafan kimiyya na Sakandare, an kuma buga su.
- Ana da littattafan kimiyya na gaba da Sakandare da na Jami’a, duk a ƙasa.
Kamar yadda na ce goyon baya da kulawa su ne suka gagara a halin yanzu.
Allah ya taimaka