Nasir I. Mahuta

HALAYE 8 DA ZASU KAIKA ZUWA GA SAMUN NASARA



1. FARAWA DA WURI: Ko kasuwanci zaka yi kada kace bari na bari sai na samu adadin kudi kaza, kawai ka fara a hankali harka kai matakin babba. Duk da yake akwai kasuwancin da suke bukatar farawa da kudi da yawa. Maimakon jira sai ka samu kudin, ka fara wata kasuwar wadda tayi daidai da karfinka. Ka sani, farawa shine gamawa. Matukar baka fara ba to ba zaka gama ba.

2. HADIN GWIWA: Komai na rayuwa yana bukatar hadin gwiwa. Koda kasuwanci kake kada kace zaka ta’allaka iya jarinka kadai, maimakon haka ka samar da alaka tsakaninka da yan kasuwar da suka fika. Ta hanyar hadin gwiwa ne kadai zaka samu karfi da tasirin da ya wuce naka. Ta hanyar hadin gwiwa ne zaka mallaki abinda yafi karfin ka. Duniyar kasuwanci tafi dogora da hadin gwiwa fiye da nuna karfin jari.

3. KA ZAMA MAI GIDAN KANKA: Duk da yake bai taba yuyuwa mutum ya zama wani ba tare da yabi ta karkashin wani ba, amma a kowanne hali idan ka samu dama kayi kokarin zama mai gidan kanka. Koda zaka tsaya karkashin wani to ya zama partnership ne. Babu laifi wani ya zama mai gidanka amma ka yi kokari akalar kasuwancinka ya kasance kaine ke juyata ba ta wani kake juyawa ba.

5. KA DAUKI DARASI DAGA KUSKURENKA: A rayuwa dole zaka yi kuskure saboda haka kada ka dauki kuskurenka a matsayin kuskure, ka dauke shi a matsayin darasi na gyara harkokinka. Duk iya karatunka kuma duk iya bincikenka wani ilimin ba zaka taba samun saba sai idan kayi kuskure.

5. KA SO ABINDA KAKE YI: Ba zaka taba maida hankali akan abinda kake yi matukar baka so abin sosai ba. Idan wani kasuwanci ko sana’a kake yi, kayi kokari kaji kana son kasuwancin sosai hakan zaisa ka maida hankali sosai. Ka ji a ranka cewa abinda kake yi yana burge ka koma kana jin dadin yinsa.

6. RAYUWA ITA CE BABBAR MAKARANTA: Ka dinga daukar darasi a cikin rayuwar mutanen da kake tare dasu yafi daukar darasi a makaranta. Idan wani ya aikata kuskure yayi rashin nasara sai ka dauki darasi. Idan wani ya aikata daidai yayi nasara sai ka dauki darasi.

7. KA ZAMA MAI DAUKAR KASADA: Aduk lokacin da tsoron yin asara yake hanaka yin abu to ba zaka taba nasara ba. Nasara tana tsakanin gwadawa da asara. Dole sai ka zama mai daukar kasada. Idan ka gwada ka yi nasara to ka samu abinda kake so. Idan kuma kayi rashin nasara to ka samu darasi.

8. KADA KA YI SAURIN WUCE SA’A: Komai yana bukatar hakuri. Kamar yadda mai noma yake farawa da sharar gona, huɗa, shuka, taki, maimai, tiri da girbi to haka kaima ya kamata ka fara komai daki-daki. Idan mai noma daga yin shuka kawai ya fara girbi to ba zai samu amfani ba karshe asarar shuka kawai yayi. To haka idan zaka yi komai kada kayi gaggawar wuce matakin da kake.

See also  TUNUBU A MATSAYIN SHUGABAN KASA (PART ONE)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button