Tambayoyi a Musulunci

SHIN ABAYA TANA DAUKAR HUKUNCIN HIJAB?Tambaya
Assalamu alaikum. Malam don Allah tambaya nake da ita kamar haka: Abaya da mata suke sanyawa tana iya daukan hukuncin Hijabi ne, domin zaka ga ko harami za ka gan su da irin wannan shigar, kuma nayi kokarin leka wasu littafai masu alaka da hijab ban iya kaiwa ga magana akan hakan ba. Malam ko akwai maganganun malamai akai? Allah ya saka maka da alkhairi.

Amsa
Wa’alaykumussalam, To dan’uwa, abin da ya wajaba ga mace musulma shi ne: ta sanya tufan da zai suturce jikinta, in ban da fuska da tafin hannu a wajan wasu malaman, wasu malaman kuma suna ganin fuska al’aura ce, don haka ita ma ya wajaba a rufe ta, tun a nan kyawun mace yake, kayan da za ta sa su zama masu kauri, ba ya halatta ta yi ado in ba a cikin gidan mijita ba, ko tare da muharramanta.

Suturar mace musulma ba’a so ta yi kama da kayan maza, kamar yadda ba’a so su zama kayan da za su ja hankali, ko wadanda aka fesa musu turare, Mutukar Abaya ko jallabiyya ta suturce jiki yadda ya kamata, ba ta matse shi ba, za ta dauki matsayin hijabin da Allah da manzonsa, suka yi umarni.

Don neman Karin bayani duba: Majmu’ul-fataawa 22\110 da Hijabul-mar’atulmuslima shafi na: 54 zuwa 67.

Allah ne mafi sani.

#Repost 15\4\2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button