NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME?
Tambaya
Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai naji daga gareka
Amsa
Wa’alaikumus salam, To dan’uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu.
Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta, da ba’a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani ba, ya wajaba ku hakurewa juna.
Don neman Karin bayani duba: Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 7\388.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
03/05/2015.