Tambayoyi a Musulunci

MANUFOFIN HUDUBAR JUMA’A



Dukkan wani aiki da ka gani a Musulunci to yana da manufa da ta sanya aka yi umarni da shi.
Kasancewar Musulmai suna haduwa duk sati ranar Juma’a, Allah Madaukakin Sarki Ya shar’anta yin huduba kafin a gabatar da Sallah, ga wasu daga cikin Manufofin hakan :

1. Yin wa’azi akan tsoran Allah da muhimmancin biyayya ga manzon tsira.

2. Koyar da mutane abin da zai amfane su daga cikin lamuran lahirarsu da duniyarsu.

3. Kwadaitar da mutane game da ayyukan alkairi da kuma tsoratar da su aikata sharri da musibar da take cikin bijirewa Sharia.

Yana da kyau malamai da limamai su ji tsoran Allah su nisanci labarai da bambadanci da huce haushi da cin fuska a mimbarin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Don neman Karin bayani duba: مقاصد الشريعة عند السعدي shafi na (318).

Dr Jamilu Zarewa
15/3/2023

See also  HUKUNCIN DAUKAR HOTO A MUSULUNCI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button