INA YAWAN SAƁON ALLAH, MENENE SHAWARA ?
Tambaya
Assalamu Alaikum. Malam a cikin zuciya ta ina jin tsoron Allah, kuma ina son bin umarnin Allah, sai dai ina yawan saɓon Allah, a taimaka min da shawara.
Amsa
Wa alaikum assalam. To, ɗan uwa ina fatan za ka karanta wannan ƙissar da idon basira, domin za ka samu shawarar da kake buƙata:
Wani saurayi ya je wajen Ibrahim ɗan Adhama, sai yace: Zuciyata tana tunkuɗa ni zuwa saɓo, kayi min wa’azi, sai yace masa: Idan ta kira ka zuwa saɓawa Allah to ka saɓa masa amma da sharuɗa guda biyar, sai saurayin yace faɗi naji:
1. Idan za ka saɓawa Allah, to ka ɓoye a wurin da ba zai ganka ba, sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’a yi na ɓoye masa alhalin babu abinda yake ɓuya gare shi? Sai yace: Yanzu ba ka jin kunya ka saɓa masa alhali kuma yana ganinka?
2. Idan za ka saɓawa Allah, to kar ka saɓa masa a cikin ƙasarsa, sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zan je alhali duka duniya tasa ce? Sai yace masa: Yanzu ba ka jin kunya ka saɓa masa alhali kana zaune a saman ƙasarsa?
3. Idan za ka saɓawa Allah to ka daina cin arzikinsa. Sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gare shi suke? Sai yace masa: Yanzu ba ka jin kunya ka saɓa masa alhali yana ciyar da kai kuma yana shayar da kai, yana ba ka karfi?
4. Idan ka saɓawa Allah, to idan mala’iku suka zo tafiya da kai wuta, kace ba zaka tafi ba Aljannah za ka. Sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, ai sun fi ƙarfina, kora ni za suyi.
5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar Alƙiyama kace ba kai ka aikata su ba. Sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, akwai mala’iku masu kiyayewa, sai ya fashe da kuka ya tafi yana maimaita wannan jumlar.
In har kana tuna ɗaya daga cikin waɗannan idan za ka aikata zunubi, to tabbas za kaji kunyar Allah.
22/12/2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa