Bincike: Yadda Za A Iya Yin Ciki Da Namiji
Babu wata tantanma ko inkarin da wani yake dashi na cewa Annabi Adamu shine mutum bil’adama na farko da Allah Ya soma turowa a wannan duniyar tamu wanda kuma bai fito kamar yadda aka saba haihuwar ko wani mutum ba.
Bisa al’ada ko dabi’a irin na mutum, kamin a haifi kowani mutum dole sai iyayensa biyu wato mace dana mijin sun yi jima’i da juna kamin cikin ya shiga har daga bisani kuma a haifi duk irin abinda Allah Ya hukunta za a haifa mace ko namiji, amma shi wannan Annabin Allah Annabi Adam shine halittan Mutum na miji na farko da Allah Ya halitta da kansa ba tare da uwa ko uba ba. Haka kuma tarihin ya tabbatar mana da cewa shine mutum na farko daya soma rayuwa da iyalinsa a bayan kasa bayan da Allah Ya fitar dashi da matarsa daga cikin gidan Aljanna.
Kamar yadda tarihi ya nuna daga shine kuma aka samu duk wata halitta na ‘yan adam da yanzu haka muke wannan duniya, shi yasa ma da bahaushe da ya tashi yiwa halittar mutum suna, sai ya kirahsi da suna Dan adam ko kuma Bil Adama a larabce.
Mata da dama dai sun fiskanci matsala na zaman aure da dama ga mazajensu ko kuma ‘yan uwan mazajensu a lokacin da suka fiskanci basa haihuwan ‘ya’ya maza.
Irin wadannan matsalolin da mata suke fiskanta kuwa sun hada da tsana da tsangwama daga wajen su kansu mazajen nasu, wani lokacin kuwa ‘yan uwan mazajen nasu, sau da dama kuwa iyayen mazajen nasu musamman surukai mata.
Sai dai kuma wani jahilcin da mafi yawan magidanta maza da mata suke fama da shi shine na rashin yarda da hukunci na Allah wanda shi Ke bada haihuwa ga wadanda yaso ya basu. Haka kuma idan Ya amince da ya bada haihuwar ma shike zabar irin abunda Ya ga dama magidanta su haifa namiji ko mace.
Bincike ya nuna cewa kashi 60 cikin 100 na matan da suka fi yawaitar haihuwar ‘ya’ya mata, ko kuma a haihuwarsu gaba daya mata suka haifa, suna cikin kunci na zaman rayuwarsu na aure saboda gazawarsu na su haifawa mazajensu ‘ya’ya maza kamar yadda mazan ko ‘yan unwan mazan ko su da kansu suke bukata.
Sai dai kuma jahilcin da masu wannan ra’ayin suke da shi game da haihuwa sun kassu kashi biyu, jahilci na farko shine na rashin yarda da hukunci Allah da kaddarar Sa na haihuwa wanda shike bayarwa ga wanda yaso a lokacin da yaso, kuma shike zabawa ma’aurata abunda zasu haifa.
Jahilci na biyu shine na rashin sanin illimin kimiya wanda ya tabbatar da cewa ita mace bata dauke da kwai halittar na miji a jikinta, ita kwai kwara daya ne a jikinta wanda idan ya hadu da wan dake jikin na miji ta hanyar fitar maniyi yakan iya rikedewa ya zama halitar data fito daga jikin na mijin ko macen bayan sun hade a mahaifa, wanda hakan ya bada damar masu illimin kimiya suka gano ta hanyar da iyaye masu sha’awar haifar jinsunan da suke bukata bin wannan tsarin.
Kwayoyi halittu biyu ne da ake gada daga wajen iyaye ga duk wani jaririn da za a haifa. Sai dai kuma akasari jarirai suna gadan ko wace kwayar halittar daga waje uwa da uba, kwaya daya daga wajen uwa daya kuma daga wajen uba.
Ita mace tana dauke ne da kwayar halitta na X har guda biyu a jikinta wanda takan iya baiwa mijinta guda daga cikin wannan kwayar halittan nata na X, shi kuma namiji yana dauke ne da halittar halittun X da Y wandanda a turance ake kiransu chromosome.
Dayake kwan halittan ‘yan adam a kimiyance suna kunshe ne da halitar X daga jikin mace ma’ana uwa kenan, shi kuma maniyin na miji mai gida kenan yana dauke da X da kuma Y wanda kuma daga nan ne ake iya samun halitar jinsi da za a iya haifa, da hakan ne kuma ya zama dole idan harma za a ga laifin rashin haihuwar da namiji ko mace a wajen uwar gida, ba ita ya kamata a daurawa laifin ba baya ga mijinta wanda she ke dauke da halitar X itace kwayar halittar da ake iya haifar ‘ya mace da shi, da kuma kwayar halittar Y wanda shine kwayar halittar da za a iya haifar na miji wanda shi namijin shike dauke dashi ba ita macen ba kamar yadda wasu ke gani.
A lokacin da mace ta sadu da mijinta kuma kwayar halittan haihuwar dake jikinta na X ya hadu da kwayar halittar X daga maniyin mijin ta, a wannan lokacin ana saran cewa idan ciki ya shiga mace zata iya haifa da izzinin Allah.
Haka kuma idan har kwayoyin halittar X daga jikin mace ya fita ya hadu da Y na mijinta, ana zaton cewa idan har ciki ya shiga namji zata haifa, duk kuwa da masu illimin kimiya sun nuna cewa shi maniyin na miji rabinsa yana dauke ne da kwayar halittun X haka kuma rabinsa kwayoyin halittar Y ne a jikinsa.
Sama da miliyan 200 ko 400 na maniyi ne yake fita daga jikin na miji a lokacin zuwan kai a cikin farjin mace, don haka idan har magidanta na bukatar haihuwar da namiji, wannan damar yana hannunsu musamman ga shi kansa mai gidan wanda shine yake dauke da kwan halittar da namiji a jikinsa.
Likita Shettles yace ga duk magidantan da suke bukatar haihuwar da namiji su kintatti sauran awa 24 kamin soma al’adar mace kana suyi jima’i ko kuma awanni 12 bayan ta gama al’ada, a cewarsa tabbas mace na iya haihuwar da namiji idan har ciki ya shiga a wannan lokacin.
Haka kuma yayi amanna da cewa, a duk lokacin da namiji yazo yin zuwan kai, idan har zai cusa azzakarinsa sosai cikin gaban mace maniyi ya shiga cikin mahaifarta kai tsaye inda kyayoyin halittun haihuwa sukan iya shiga su makalle cikin cikin mahaifar, hakan kuma yakan baiwa kwayar halittar Y ya samu rayuwa a cikin mahaifa ganin yafi kwayar halitta na X jimawa a raye.
A lokacin da kwayar halittar X da X suka shiga mahaifar mace, a wannan lokacin ne ake iya haifar tagwaye ‘ya’ya mata, haka kuma idan Y da Y sune suka samu shiga mahaifar, nan ma ‘yan tagwaye maza za a iya haifa, ko idan X da Y suka shiga a samu ‘yan takawaye mace dana miji.
Ita ma likita Whelan, tace mutum yace zai zabawa kansa irin dan daya keso ya haifa abune mai wuyar gaske, sai dai kuma a cewarta muddin za a sadu da mace daf da lokacin da zata soma al’ada ko kuma ‘yan awanni da bayan gamawarta, tana da tabbacin cewa idan ciki ya shiga ana iya haifar da namiji.
Idan mukayi la’akari da wadannan nazarorin da likitoci suka yi, zamu fahimci cewa ita mace bata da laifi a duk wani abunda take haifa, domin kwan halitta dai yana jikin namiji ne, ita kawai sai dai ta kenkeshe abunda aka sanya mata a cikin mahaifarta amma bata da tasirin wajen sako halittar da za a iya haifa kamar shi mijinta.
Da wannan bayanin da likitocin suka yi ne bayan binciken da suka gudanar, suke ganin cewa ga duk wasu magidanta da suke sha’awar haihuwa ‘ya’ya maza, muddin zasu bi wannan nazarain nasu suna ganin cewa suna iya haihuwar ‘ya’yansu maza a duk lokacin da suke bukata.