Abunda Ke Jawo Azzakari Girman Wuce Kima
Tsangayar Malam Tonga
Kamar yadda aka sani, madaidaicin azzakari bai wuce inci 5 zuwa 7 ba idan yana mike. Duk azzakarin daya haura hakan masana suna ganin ya wuce kima.
Duk dayake, ana samun masu ikirarin suna da magunguna na kara tsawo ko kaurin azzakari a likitance da al’adance, sai dai masana sunce babu wani tabbas a wannan ikirarin.
Sai dai kuma, bincike ya gano cewa, akwai wasu hanyoyin da azzakarin maza yake iya girma ko tsawon wuce misali.
Hanya na farko shine gado. Akwai mazan da haka nan zuriyansu suke da makeken gaba. Duk namijin da aka haifeshi cikin iyayensa da kakaninsa suke da wadatar azzakari yana iya tasowa shima da hakan.
Hormonal Influence wani sinadari ne da yake samuwa daga jikin namiji musamman namijin da yake da girman ‘ya’yan maraina.
A lokacin balagar namiji, idan har yana da wannan sinadarin a tare dashi da akwai yiwuwar gabansa ya zama mai kauri, tsawo.
macrophallus da kuma megalophallus wasu sinadare ne a jikin namiji da suke sa gaban namiji yayi girman wuce misali.
Hakan kuma na samuwa ne a lokacin da namiji ya soma girman balaga, a wannan lokacin ne yake iya samun wannan sinadarin yake shiga jikinsa.
Akwai kuma wasu al’adun da mutane suke da shi na baiwa duk wani da namiji wasu jikon da yake sa gaban namiji ya kara girma.
Wadannan sune abunda bincike ya gano suna iya sa gaban namiji ya kara girma fiye da kima. Kuma a lokacin tasowar sa na balaga.
Amma idan kana sha’awar naka ya kara girma da girmanka a yanzu. Akwai wasu hanyoyi da magungunan da ake dasu domin gwaji ko za a dace.