Tambayoyi a Musulunci

MA’AIKACIN ZABE, ZAI IYA AMSAR KYAUTA DAGA JAM’IYYU !Tambaya
Assalamualaikum, Malam meye hukuncin kudin da jam’iyyu ke ba malaman zabe a lokacin zabe ? alhali su malaman zaben hukumar zabe za ta biya su kudin aikinsu?

To malam kasan kowa da account number din shi a wurinsu, jiya bayan na dawo gida sai aka min alert na kudin rumfar !

Amsa
Wa alaikum assalam,
Wannan kudin da kuke amsa haramun ne kuma cin hanci ne, saboda an ba ka ne saboda kujerarka ta ma’aikacin zabe, inda a gidanku kake da ba su ba ka ba.

Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Abu-dawud ya rawaito “Duk wanda muka sanya shi wani aiki sannan muka yanka masa albashi akan aikin, to duk abin da ya karba bayan haka wuta bal-bal ya ci”.

Annabi S.A.W. ya fusata sosai kuma ya yi maganganu masu kaushi lokacin da ya aika IBNU-ALLUTBIYYA karbo zakka amma kuma sai aka ba shi kyauta ya karbe kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

Hadisan da suka gabata suna nuna cewa: haramun ne ma’aikacin da yake da albashi ko alawus ya amshi kyautar da aka yi masa saboda aikinsa, in har ya amsa kuma to ya ci rashawa.

Idan ma’akaicin zabe ya karbi kyauta daga jam’iyyu, magudin zabe ba zai yi wahala ba, daga cikin salon magana a harshen Hausa “Duk Wanda ya mika hannu ba zai iya mike kafa ba” wannan yasa Musulunci ya haramta irin wannan Ihsanin.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa
17/03/2023

See also  HIKIMOMIN DA AZUMI YA ƘUNSA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button