Tambayoyi a Musulunci

BA YA HALATTA KA YI VIDEO CALL DA MATARKA !


Tambaya
Salamun alaikum,
Malam idan na Yi tafiya zan iya Kiran matata ta WhatsApp ta cire kayanta mu Yi waya, na ganta, saboda na samu saukin sha’awar da take damuna ?

Amsa
Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda kamfanin WhatsApp da hackers da Injiniyoyi in sun so za su iya ganinku, Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi Yana cewa: “Ka kiyaye al’aurarka in ba ga matarka ba da kuma abin da damarka ta mallaka”, Kamar yadda Abu dawud ya rawaito a hadisi ingantacce.

Kasancewar What’sapp babu sirri, Vidio call na tsaraici ya zama haramun, Annabi (SAW) ya kasance ko bukata zai biya yana yin nesa da sahabbansa, da inda mutane ba za su gan shi ba, Kamar yadda Ibnulkayyim ya ambata a Zadul ma’ad 1/171.
An rawaito cewa Yana cikin damuwar Nana Fadima ranar da za a dauke ta a Makara, saboda maza za su iya hangarta a rufe cikin likafani, Kamar yadda Hakim ya rawaito a Mustadrak da Abu Nu’aim a Hilya.

Dalilan da suka gabata suna nuna cewa Haramun ne mutum ya cusa kansa wurin da za a iya tsikayo a al’aurarsa in ba wuraren lalurar da Sharia ta togace ba.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
19/07/2022

See also  MIJINA MAZINACI NE, ZAN IYA JUYA MASABAYA?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button