AdSense

Menene Google Adsense, Ya Ake Amafani Dashi, Taya Ake Samun Kuɗi Dashi Ta Hanyar Rubutu?Nasan kana yawan jin ana maganar Google Adsense ko kaji ana cewa ai idan ka buɗe Channel a Youtube Google Adsense zasu dinga biyanka, ko kuma idan ka buɗe Website shima Google Adsense zasu dinga biyanka da sauransu, kai kuma ƙila har gobe bakasan ma menene Google Adsense ɗin ba, bare ma kasan taya zasu biyaka, taya ma zaka samu kuɗin ko taya zaka ƙulla kasuwanci dasu da sauransu, Insha Allah zanyi taƙaitaccen bayani akan sanina da Google Adsense da yadda ake samun kuɗi dashi ko ake amfani dashi ake samun kuɗi.

Google Adsense wani ƙyaƙyƙyawan tsari ne da aka samar wanda yake ƙarƙashin kamfanin “Google” an ƙirƙiri Google Adsense ne saboda masu rubutu a yanar gizo ko wanda suke amfani da shafukan yanar gizo, “Google Adsense” yana amfani ne ta hanyar nuna tallan kaya ta ɓangare daban-daban yakan iya fitowa a siffar rubutu, (Notes) hoto (Pictures) ko kuma hoto mai motsi (Videos).

Yana aiki ne ta hanyar nuna talla a sifar hoto, rubutu ko kuma hoto mai mosti (video) shafin yana ɗaya daga cikin manya kuma sanannun shafuka wanda suke taimakawa mutane masu rubutu a yanar gizo domin samun kuɗi, mutum yakan samu kuɗi na asali a yanar gizo ta hanyoyi daban-daban wanda nayi bayanin su a cikin littafina (PDF) mai suna “FreeLancing Guide 01”, sai dai duk hanyoyin basa zuwa cikin sauƙi suna buƙatar aiki tuƙuru kamar dai komai a rayuwa bazaka zauna jiran kuɗi yazo neman ka ba sai dai ka fita ka nemi aiki dan samun kuɗin kashewa haka zalika shima aiki a yanar gizo.

A gaskiya wannan tsarin na Google Adsense ba sabuwar hanya bace an jima ana samun kuɗi a yanar gizo da ita sai dai yawanci mutanen mu basu san dashi ba amma wasu shafukan suna amfani dashi misali kamar BBC Hausa, Daily Nigerian, da sauransu, a duk sanda muke buƙatar sanin wani abu a yanar gizo mukanyi ƙoƙarin dubawa a “Google Search” wajen neman sa musamman idan ya shafi harkar boko, ko makamantanshi yanzu misali idan muka shiga Google mukayi Search ɗin “Yanda ake samun kuɗi a Internet” in har da harshen turanci zamu duba wannan Kalmar a yanar gizo zamuga cewa shafuka sama da ɗari ne zasu bamu amsar wannan tambayar amma shin ka taɓa tambayar kanka meyasa ba shafi ɗaya kawai ya kamata a samu wannan amsar ba,?

Meyasa shafuka da dama zasu bamu amsar tambayar mu?

To a zahirin gaskiya zan iya faɗan cewa yawancin duk shafukan da zakaga ana rubutu da harshen turanci ana yin su ne saboda kuɗi kuma Alhamdullilah suna samu shine gaskiyar maganan, Google Adsense Yana ɗaya daga cikin manyan hanyoyi da ake bi wajen samun kuɗi a yanar gizo, za’a samu kuɗi ne ta hanyar sanyasa a shafin rubutu na “Blog ko Website, za ka iya zaban nauo’I daban daban na girma wanda ya dace da shafinka sannan ka samar da wani code wanda zaka sa a shafinka dan nuna tallace tallace, zaka samu kuɗi ne ta hanyar amfani da google adsense kawai idan har mutum ya shiga shafinka kuma ya danna wannan tallace tallace da akeyi a shafinka. Google Adsense suna amfani da sakago (roboot) wanda sukan karanta abunda kake rubutawa a shafinka koda wani kalan yare ne, sannan zasu samar da talla wanda ya dace da abinda kake rubutawa sai su saka a website ɗin ko youtube ɗin ba lallai bane su saka abinda ranka ke so sai dai baza su nuna kayan tsiraici, batsa ko abu makamancin haka ba.

“Google” kamfanine da suka wuce tsanmanin ka saboda suna da ma’aikata sama da 50 a kowace kasa a faɗin duniyan nan dan haka samun kuɗinka ba abun damuwa bane kawai dai bisa dokar su dole sai kuɗinka ya kai dala 100 wato $100 wanda ya kama naira dubu talatin da shida N 3600 a yanda canji dala yake a yau ba lallai ya zauna a haka ba zai iya fin haka ko kuma ya zama kasa da haka saboda ya danganta ne da canjin dala, suna tura kuɗi a hanyoyi guda biyu a nan Nigeria, na farko shine ta hanyar “Cheque” wanda suke turawa ta hanyar sako, zasu ba ɗaya daga cikin ma’aikacinsu ya kawo maka har gida in dai kana cikin gari a kowace jaha a cikin faɗin duniyar nan kuma zasu kawo maka kuɗin ne a Dollars kai kuma sai kaje banki a canza maka zuwa kuɗin kasarka Nigeria wanda zai iya ɗaukan yan wasu ƙwanaki.

Sai hanya ta biyu shine banki, sukan iya turama kai tsaye zuwa account naka dake banki in dai ka cika sharruɗan su wanda zanyi bayaninsu nan gaba.

Babban kalubalen da zan iya cewa zaka fuskanta da farko shine wajen amincewa da shafinka, a zaharin gaskiya a yanzu Google Adsense basu karɓan shafukan da ake rubuta su da harshen hausa, ba ma hausa kaɗai ba har wasu harsunan ma, suna karɓan harsuna guda sha ɗaya ne kacal duk faɗin duniyan nan wanda ya haɗa da turanci amma wannan ba mastala bane in dai ka iya rubuta abu mai ma’ana da harshen turanci zasu iya karɓanka Idan Allah yasa ka samu karɓuwa a shafin naka na turanci zaka iya amfani dashi a kowani irin yanayi koda kuwa yana ɗauke da wani yarene wanda basu amince ba sai dai kawai karka sa abinda basa buƙata, Misali Abubuwan batsa, iskanci, yanda ake sace kayan wani ko wata, yanda ake hac-king da dai sauran wasu kayan almundahana wanda basu dace ba.

Sai mun haɗu wani karon, Allah yataimake mu.

Salisu Abdurrazak Saheel

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button