Zikirin safe da maraice
ZIKIRIN SAFE DA MARAICE
An Karbo daga Anas (RA) lallai annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya fada a lokacin da ya wayi gari, ko a lokacin da ya yi yammaci:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ وَمَلَائِكَتَكَ، وَجَمِيعَ خَـــلْقِكَ أَنَّـــكَ أَنْـــــــــــــتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُكَ وَرَسُولُك».
Ma’ana: “Ya Allah lallai ni na wayi gari ina shaida maka, kuma ina shaida ma mala’ikun da su ke dauke da al’arshinka, da sauran mala’ikunka, da sauran halittunka gabadaya cewa: Lallai kai ne Allah wanda babu abun bauta da gaskiya sai kai, kuma lallai Muhammadu bawanka ne kuma manzonka ne”. Wanda ya fadi haka Allah zai yanta daya bisa hudunsa (1/4) daga wuta, Wanda kuma ya fade shi sau biyu Allah zai yanta rabinsa ne, wanda kuma ya fada sau uku to shi kuma Allah zai yanta uku bia hudunsa (3/4) daga wuta, In kuma ya fada sau hudu to Allah zai yanta shi gabadayansa daga wuta”. Abu-dawud ya rawaito shi da isnadi mai kyau (hasanan). Da An-nasa’iy a cikin littafinsa “amalul yaumi wallailah”, da Isnadi hasanan, Lafazinsa kuma shi ne:
«مَنْ قَالَ حِينَ يُصْبِحُ: اللَّهُمَّ إِنِّي أَصْبَحْتُ أُشْهِدُكَ وَأُشْهِدُ حَمَلَةَ عَرْشِكَ، وَمَلَائِكَتَكَ وَجَمِيعَ خَــــلْقِكَ، أَنَّــكَ أَنْتَ اللَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، وَحْدَكَ لَا شَرِيكَ لَكَ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُكَ وَرَسُولُكَ، أَعْتَقَ اللَّهُ رُبُعَهُ ذَلِكَ الْيَوْمَ مِــــــنَ النَّارِ، فَإِنْ قَالَ أَرْبَعَ مَرَّاتٍ أَعْتَقَهُ اللَّهُ ذَلِكَ الْيَوْمَ مِنَ النَّارِ».
Ma’ana: “Duk wanda ya fada a lokacin da ya wayi gari: Ya Allah lallai ni na wayi gari ina shaida maka, kuma ina shaida ma mala’ikun da su ke dauke da al’arshinka, da mala’ikunka, da sauran halittunka gabadaya cewa: Lallai kai ne Allah wanda babu abun bauta da gaskiya sai kai; kai daya ka ke baka da abokin tarayya. kuma lallai Muhammadu bawanka ne kuma manzonka. = Allah zai yanta daya bisa hudunsa (1/4) a wannan yinin daga wuta, In kuma ya fada sau hudu to Allah zai yanta shi a wannan yinin gabadayansa daga wuta.