Tambayoyi a Musulunci

AN BIYA MIN AIKIN HAJJI SAI MJINA YA MUTU, SHIN ZAN IYA TAFIYA ?



Tambaya:
Salamun alaikum. Allah ya taimaki Malam, an biya min aikin Hajji sai mijina ya mutu, shin zan iya tafiya?

Amsa:
Wa alaikum assalam. Allah yayi masa rahma. Ba za ki tafi ba, saboda Allah ya umarci wacce take takaba a Suratul Baƙara da ta zauna a gida, kar ta fita.
Idan mace ta tafi aikin Hajji sai mijinta ya rasu bayan ta isa Makkah za ta ci gaba da aikinta, ba za ta tsaya ba ko ta dawo, saboda ƙa’idar: الدفع أسهل من الرفع, “tunkuɗe abu kafin a fara ya fi sauƙi akan tunkuɗe shi bayan an tsunduma.

Allah ne mafi sani.
28/06/2022
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  HUKUNCIN KASHE KWADI DA CIN NAMANSU

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button