Tarihin Sayyidina Umar

TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA 4

Ƙaunar Da Sayyadina Umar (RA) Yakewa Ahlulbaiti

A cikin Wadanda Umar ya ke yi wa rajistar, ya tarar da sunayen Hassan da Hussaini a matsayinsu na ‘ya’yan Sayyadina Ali (AS) dai dai da sauran ƙananan yara ‘ya’yan Sahabbai, suna da dirhami dubu biyu ko wannensu. Amma sai Sayyiduna Umar ya cire su, ya riskar da su da babansu, aka yanka masu dubu biyar-biyar, ya ce, saboda kusancinsu da Manzon Allah da irin son da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ɗin yake yi masu.

“Abdullahi ɗan Umar ya yi koke game da nasa albashin, domin Sayyiduna Umar ya ƙara ma Usamatu ɗan Zaid Dirhami ɗari biyar a kan albashinsa. Shi kuma a ganinsa, ba wani abinda ya raba shi da Usamatu, domin su tsara ne, waɗanda suka tashi tare, suka je wuraren jihadi ɗaya Sa’oi Ne da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Amsar da Babansa ya ba shi ita ce: “Na fifita shi ne a kanka, don Manzon Allah ya fi sonsa a kanka, ya kuma fi son mahaifinsa a kan naka”

“A cikin matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ma, sai da Umar ya fifita Nana Sayyada A’isha (RA) a kan sauran mata (waɗanda suka haɗa da ɗiyarsa Hafsah), la’akari da fifikonta wajen son da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ke yi mata. Duk da ya ke wasu kan cewa, tun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai banbanta su ba a kyautukansa, shi ma ya daidaita su. Sa’annan ya mayar da albashinsu iri ɗaya.”

“Idan mu ka koma wajen sauran dangin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, za mu ga irin matsayin da su ke samu a wurinsa. Misali, Umar ne kaɗai a zamanin mulkinsa ya ke kusanto da ƙanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Abdullahi ɗan Abbas, duk da ƙanƙantarsa. Idan aka yi masa magana ya kan ce: “Yaro da gari abokin tafiyar manya ne”. Ya na nuni da irin ilminda ya ke da shi”

See also  TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA SHIDA (6)

“Game da mahaifin nasa kuma (Ina nufin Abbas, baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama) Umar ya taɓa yin Riskar da fushinsa. Wannan ya faru a lokacin da aka ci garin Makkah, domin shi Umar ɗin ya na da ra’ayin duk a gama da maƙiyan musulunci waɗanda suka ƙare rayuwarsu wajen yaƙar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi kuma Abbas ya na da ra’ayin a yafe masu. Da zancen ya haɗa su sai Abbas ya fusata, ya ce, don dai ba ‘yan ƙabilarka ba ne! Anan sai Umar ya ce masa, Ni, ba ni da wani ƙabilanci ga jama’ata a kan musulunci. Don wallahi ranar da ka musulunta nafi farin ciki bisa ga a ce khaɗɗabi ne, babana, ya musulunta, don kuwa na san irin farin cikin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan musuluntarka”.

Yadda Umar Yake Kula Da Dukiyar Jama’a

Umar ya kasance mai yawan tsentseni dangane da dukiyar al’umma da yake kula da ita a matsayinsa na shugaban Musulmi. Kuma ya kan tsananta ma kansa da iyalansa dangane da ita. Ga wasu daga cikin labaran irin taka tsantsan da yake yi:

  1. Umar ya kan kashe fitilar gwamnati idan ya ƙare aikinda ya shafi jama’a sannan ya kunna tasa domin kada ya shiga haƙƙen da ba nasa ba.
  2. A lokacin da yaronsa ya ba shi madara ya sha yana tsammanin daga raƙumarsa ne, amma daga baya ya gane daga raƙumar gwamnati ne sai da ya shawarci surukinsa Sayyiduna Ali a kan wannan, Ali ya nuna masa ba kome.
  3. Ya samu labarin ɗansa ya kiwata raƙumarsa a cikin raƙuman gwamnati, sai ya hane shi kuma ya umurce shi da ya mayar da abin da ta haifa a cikin taskar gwamnatin tun da yake da abincin gwamnati aka yi kiyonta.
  4. Matarsa Ummu Kulsum ɗiyar Sayyiduna Ali ta aika da kyautar turare zuwa ga matar sarkin Ruma ta hannun Manzon da ya aika masa. Da aka zo mata da tukuici sai ya umurce ta da ta mayar da shi cikin dukiyar gwamnati tun da yake Manzon da ya kai saƙon gwamnati ce ta aike shi. Da ta kai ƙara wurin mahaifinta, Sayyadina Ali (RA) ya goyi bayan khalifa Umar, sai dai ya ba da shawarar a cire ma ta daidai abin da ta aike da shi.
  5. Ya kan hana matansa su yi amfani da abin da ya rage idan aka raba Turare ko Mai ko ire irensa ko da kuwa su shafa kansu da abinda ya saura a hannayensu ne domin yana ganin ba halaliyarsu ba ne.
See also  TARIHIN SAYYADINA UMAR IBN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU KASHI NA 3

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button