RamadanTambayoyi a Musulunci

NA YI JIMA’I A RAMADHANA, AMMA BA ZAN IYA KAFFARA BA ?Tambaya:
Assaalamu Alaikum Dr., Ina da tambaya game da Hadisin Manzon Allah (S.A.W.) akan wani mutum da ya sadu da matar sa da rana cikin Ramadan, duba da yadda Manzon Allah ya warware masa matsalarsa, to idan har an sami wani ya sadu da matarsa da azumin kuma ba zai iya Azumi, ƴanta wuyaye ko ciyarwa ba, kuma bai sami wanda zai ba shi abin da zai ciyar ba, yaya zai yi?

Amsa:
Wa alaikum assalam. To ɗan uwa, ƙissar da ka faɗa ta zo a Hadisi tabbatacce mai lamba ta (616) a cikin Sahihil Bukhari, saidai Malamai sun yi saɓani akan abin da ka tambaya zuwa zantuttuka guda biyu:

1. Kaffarar ba za ta faɗi a kansa ba, za ta wanzu har zuwa lokacin da zai samu damar yin ɗaya daga cikinsu, kamar yadda suke a jere a Hadisin, saboda Annabi (S.A.W.) a cikin Hadisin bai ce masa kaffara ta faɗi a kansa ba, yayi masa shiru ne.

2. Kaffarar ta faɗi akansa, saboda lokacin da ya ce ba zai iya ba, Annabi (S.A.W.) ya bar masa dabinon don ya ciyar da iyalansa.
Wasu Malaman suna rinjayar da zance na ƙarshe, saboda shine ya fi dacewa da zahirin Hadisin.
Don neman ƙarin bayani, duba: Al-minhaaj na Nawawy 3/182-183.
_Allah ne mafi sani._
06/07/2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

See also  TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA!!!

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button