Tarihi

Farkon Karatun Ƙur’ani a rediyo

A 1951 gwamnatin mulkin mallaka ta kafa gidan rediyon NBS a Legas tare da rassansa a Ibadan da Inugu da Kaduna. Tun a 1932 dai aka fara sauraron rediyo a Najeriya bisa tsarin RDS, amma baki ɗayan shirye-shiryen na Ingilishi ne zalla. Don haka aka kafa NBS saboda a fara gudanar da shirye-shirye a Najeriya kuma cikin harsunan ’yan ƙasa.

Wannan gidan rediyo na NBS shi ne ya fara saka karatun Alƙur’ani Mai girma a tasharsa da ke Kaduna. Sai dai hakan ya jawo ce-ceku-ce. Domin kuwa Musulmi da ke Arewacin Najeriya sun koka da suka ji karatun Kur’ani a cikin na’ura ta ‘sharholiya’ irin rediyo wadda aka saba jin kaɗe-kaɗe da kuma zantuttukan duniya a cikinta. Don haka suka yi ta rubuta wasiƙun ƙorafi zuwa ga gidan rediyon inda suka buƙaci a daina sa Kur’ani saboda yin hakan tamkar wulaƙanta shi ne.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi shi ne Shugaban Hukumar Daraktocin Gidan Rediyon a wancan lokaci. Don haka a wurinsa shugabannin gidan rediyon suka nemi mafita.

A 1954 Sarki Sanusi ya dakatar da saka karatun Kur’ani a rediyo, inda ya nemi fatawa daga malaman Tijjaniya na Kano da kuma Sarkin Zazzau Ja’afaru ɗan Isiyaku, wanda shi ne wanda ake gani ya fi kowanne Sarki a Arewacin Najeriya ilimin addini a lokacin. Malaman Kano sai suka aike da fatawar zuwa ga Shehinsu Ibrahim Inyass. Amma sai baki ya rabu biyu. Shehi Inyas ya ba da fatawar cewa saka karatun Kur’ani a rediyo ya halatta yayin da Sarkin Zazzau Ja’afaru ya ce tunda yake babu wani nassi ƙarara da ya bayyana halacci ko haramcin saka Kur’ani a rediyo, yana ganin gara kada a sa saboda kada a buɗe ƙofar keta alfarmar Littafi Mai girma.

See also  Tarihin Musulman Japan Da Musulunci a kasar Japan

Ganin an samu wannan saɓani sai ɗaliban Inyas na Kano suka tura masa da fatawar Sarkin Zazzau. Daga nan ya rubuto littafi mai taken Al-Hujja al-Baligha fi Kaunil Iza’atil Kur’ani Sa’igha, inda a nan ya yi cikakken bayani tare da kawo gamsassun hujjoji cewa sa karatun Kur’ani a rediyo ko bai kai matsayin wajibi ba, ya kai matakin halal abin so. Bayan samun wannan fatawar ce aka ci gaba da saka karatun Alƙur’ani a rediyo.

Tafsiri a Rediyo

A 1962, Rediyon NBC Kaduna ya fara sa karatuttukan tafsiri na malamai da ake naɗa a kasakasai na rikoda. Malaman sun haɗa da Modibbo Jilani Yola da Malam Baba Sakkwato da Malam Tijjani Usman Zangon Barebari da Malam Nasiru Kabara daga Kano. Amma dai jefi-jefi ake sa wa kuma ba lallai sai cikin watan Ramadan ba. Sai a 1967 ne aka fara saka karatun tafsiri cikin watan Ramadan a gidan rediyo na NBC Kaduna. Karatun da aka fara sakawa shi ne wanda Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yake gudanarwa a Masallacin Sultan Bello.

Saɓanin sauran malaman da suke tafsiri, shi ba ya ɗariƙa, hasali ma babban aikin da ya sa gaba shi ne sukar aƙidun ’yan ɗariƙu.
Koda yake tun 1962 yake gudanar da tafsiri a Masallacin Sultan Bello, lokacin da aka fara sa shi a rediyo sai ya fara sassautawa saboda a cewarsa babu damar amsa tambayoyin waɗanda ba su fahimce shi ba.

A 1967 ne kuma gwamnatin mulkin soja ta Janar Gowon ta ƙara jihohin Najeriya daga huɗu zuwa 12. Don haka jihohi shidan da ke Arewa su ma kowace ta buɗe gidan rediyo sai ta samar da gurbin karatun Tafsiri. Amma a Rediyon Najeriya Kaduna, wacce ita ake ji a duk faɗin Najeriya dama wasu daga cikin ƙasashen waje, Sheikh Abubakar Gumi ne kaɗai ke yin tafsiri tsawon shekara 10 daga 1967 zuwa 1977.

See also  Tarihin Hudhayfa ibn al-Yaman

A cikin watan Maris na 1977 ne ƙungiyoyin ’yan Dariƙar Tijjaniya da suka haɗa da Fityanul Islam da Dakarun Ɗan Fodiyo da Jama’atu Ahlis Sunnah suka gudanar da zanga-zanga a Birnin Kaduna inda suka roƙi gwamnati da gidan rediyon su dakatar da tafsirin Sheikh Abubakar Gumi. Sakamakon haka Mataimakin Shugaban Kasa na mulkin Soji Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’adua ya umarci gidan rediyon ya ci gaba da karatun Gumi amma ya bai wa wani malamin Tijjaniyya dama. Don haka aka zaɓo Sheikh Umar Sanda Idris, mutumin Zariya mazaunin Kaduna ya cike wannan gurbi.

Ya kuma gudanar da tafisrin tsawon shekara uku daga 1977 zuwa 1979 amma a tsittsinke saboda a ranaku da yawa ma’aikatan rediyo kan ce ba za su samu kawo shirin ba saboda tangarɗar na’ura. Shi kuma salon karatunsa ba irin na rediyo ba ne. Irin dai wancan tafsirin ne na asali wanda malamai suke yi tsakaninsu da ɗalibansu. Domin kuwa a cikin watannin azumi guda uku bai kammala tafsirin Suratul Fatiha ba, saɓanin Sheikh Gumi da ke kammala ta cikin minti 20. Wannan ya sa tafsirin bai ja hankalin masu sauraro ba.

Don haka Kungiyar Fityanul Islam sai ta sayi fili a rediyo aka fara saka karatun Sheikh Zubairu Surajo. Shi kuma kafin watan ya ƙare sai ya tafi Umara inda ya bar Malam Mahmud Umar ya ci gaba. Cikin ikon Allah sai karatun Malam Mahmud ya fi karɓuwa.

Don haka da Malam Zubair ya dawo daga Umara sai Malam Mahmoud ya ƙi sauka daga kujerar. Wannan ya sa a 1979 aka gudanar da tafsiri guda huɗu a Rediyon Najeriya na Kaduna; Uku daga ɓangaren Tijjaniya ɗaya daga ɓangaren Izala.

See also  TARIHIN SHIEKH MUHAMMAD NASURUDDIN ALBANI. مُحَمَّد نَاصِر ٱلدِّيْن ٱلْأَلْبَانِي الأرنؤوط)

Bayan azumin aka samu sulhu a Tijjaniya inda aka ɗauko Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda dama ana sa tafsirinsa a gidan rediyon Bauchi ya dawo Kaduna. Nan take Malam Umar Sanda ya yi ritaya daga tafsirin rediyo amma Fityanu ba ta amince ba.

Don haka aka ci gaba da tafsirin Malam Mahmud Umar daga Masallacin Juma’a na Kano Road da Sheikh Dahiru Bauchi daga Masallacin Tudun Wada sai kuma Sheikh Abubakar Gumi daga Masallacin Sultan Bello.

Shi ma Sheikh Dahiru Bauchi yana cikin waɗancan malamai ’yan ƙablu da suka yi karatu a Kaulaha wurin Sheikh Ibrahim Niasse tun cikin shekarun 1940. Inda salon tafsirinsa ya bambanta da kowa shi ne ba ya duba wani littafi sai dai ya riƙe carbinsa.

Tun daga wancan lokaci ɓangarorin biyu suke amfani da wajen tafsiri wurin sukar juna da mayar wa da juna martani.

Daga Maude Rabi’u Gwadabe
Saliadeen Sicey ✍️

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button