Tambayoyi a Musulunci

BA ZAI YIWU A KAFIRTA DUKKAN ‘YAN SHI’A BA !Tambaya
Assalamu alaikum, ina yiwa malam fatan alkairi, Allah ya hadamu a Aljannar da koramu suke gudana a cikinsa, tambayata shi ne: Don Allah malam wanne abubuwa ne wanda ‘yan Shi’a suke aikatawa wanda ya fitar da su daga musulunci ?

Amsa:
To dan’uwa tabbas a cikin addinin shi’a akwai manyan abubuwa wadanda suke warware musulunci:
1. Daga ciki akwai zagin mafi yawancin sahabbai, tare da cewa, Allah ya tabbatar da cewa ya yarda da su a ayoyi da yawa a cikin alqu’ani, duk wanda ya ce mafi yawancin sahabban Annabi ﷺ sun kafirta tabbas ya karyata Allah, wanda ya karyata Ubangiji hukuncinsa a fili yake.
2. Yana daga cikin akidunsu tabbatar da cewa: Alqur’anin da yake hannunmu bai cika ba, tare da cewa: Allah ya tabbatar: zai kiyaye shi, har abada.
3. Suna riya cewa: an yi kuskure wajan baiwa Annabi ﷺ Annabta, sayyadi Aliyu ya kamata a bawa, sai mala’ika Jibrilu ya yi kuskure ya bawa Annabi Muhammad ﷺ, tabbas wannan maganar ta kunshi nuna gajiyawar Allah da kuma karyata shi.
4. Rafidha ‘yan shia sun tafi akan cewa Nana A’isha Mazinaciya ce, tare da cewa Allah ya kubutar da ita daga abin da munafukai suka zarge ta da shi a ayoyi guda goma a suratun Nur.

Ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za’a kira shi da kafiri, dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.

Yana daga cikin ka’idoji a wajan malaman AHLUSSUNNAH ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin ‘yan shi’a da gama-gari wadanda suka shiga shi’a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirata su ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa da suka gabata, saboda akwai hadisai da yawa wadanda suke bawa wanda ya aikata kafirci da jahilci uzuri, amma wanda ya aikata daya daga cikin su da ilimi to malaman musulunci da yawa sun dora masa KAULASAN.
Don neman Karin bayani duba: Ashshifa’a Na Kadhi IYadh 2\286 da Al-kifaya: 67.
Allah ne mafi sani.

24\12\2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button