BA KOWACCE “ALLAH YA ISA” TAKE TASIRI BA !
Tambaya
Assalamu Alaikum, Allah Ya Gafarta Malam, Uba Ne A Cikin Gida Duk Hakkokin Dake Kan Shi Na Iyalan Shi Baya Saukewa, Sai Matar Ce Take yin Komai, Kama Daga Cin Yara, Suturar Su, Dawainiyar Makaranta Da Sauran Su, Sai Rannan Wata Yar Hatsaniya Ta Shiga Tsakanin Su, Sai Yace Duk Abunda Ta Kara yi A Gidan Wanda Yake Hakkin Shi Ne Allah Ya Isa Bai Yafe Mata Ba, Kuma Malam, Bayyi Idan Ta Bari Yayan Ta Zasu Galabaita Su Shiga Ukku, To Malam Idan Taci Gaba Dayi Allah Ya Isan Shi Zata Bi Ta? Nagode
Amsa Wa alaikum as salam,
Ya wajaba ya ciyar da su, in kuma ya kı sai ta Kai shi wajan alkali, tun da ciyar da iyalai wajibı ne akan Uba mutukar yana da iko, Hindu bintu Utbah ta je wajan Annabi s.a.w. ta fada masa cewa: mijinta Abu Sufyan marowaci ne ba ya bata abin da zai ishe ta, ita da iyalanta, sai Annabi s.a.w. ya ce mata : Ki dauki abin da zai işhe ki ke da yaranki dağa dukiyarsa. Buhari ne ya rawaito.
Idan kuma ba shi da halı kına iya ciyar da su, “ALLAH YA ISAN SHI” ba za ta cutar da ke ba, saboda ba kowacce adduar sharri Allah yake amsa ba, ında Allah yana amsar dükkan addu’o’in sharrin da mutane suke yi, da sun hallaka sun kare, kamar yadda aya ta : 11 a suratu Yunus take nuni zuwa hakan.
Allah ne mafi Sani
Dr. Jamilu Zarewa
20/11/2015