ComputerTech

MATAKAN DA AKE BI WAJEN KOYAN COMPUTER


Daga bakin masana computer na Arewa-webmasters

Kasancewar computer a matsayin wata aba wacce amfani da ita ke kara zama kamar ruwan dare ne garwaye duniya, koyonta da kuma iya amfani da ita a ko da yaushe yana kara zama wajibi a wajen mutane saboda irin alfanun da take da shi. A lokuttan da suka gabata, mutane da yawa na  alakanta ilimin computer ne da abubuwan da suke da alaka da ita kai tsaye ta hanyar aiki ko kuma a ilimance. Sabanin lokutan baya da amfanun computer bai yawaita ba, a wannan lokacin da muke ciki, amfanin computer ya wuce misali, ta yanda amfani da ita ya zama kusan dole a kusan ko wane irin fanni da kuka sani na rayuwarmu. Sakamakon haka ne ya sanya a ko wace rana bukatar koyon wannan ilimi mai matukar muhimmanci yake kara baiyanuwa. To amma babbar tambaya da mafi yawanci masu bukatar koyon wannan ilimi na computer kan yi a ko da yaushe ita ce, shin ta ina ya kamata mutum ya fara? A cikin wannna kasidar ta musamman, zamu yi cikakken bayani akan inda mutum ya kamata ya fara da kuma abubuwan da ya kamata ya yi a lokacin da yake koyon wannan ilimi.

Kasancewar a yanzu computer ta shafi fannoni da dama, wanda kuma wasu daga cikin wadannan fannonin suma sun kasu ya zuwa wasu fannonin, ba zaya taba yiyuwa ba mutum ya iya koyon duk wani ilimi na computer. Ga dukkan mai son samun nasara akan koyon ilimin computer, to ya zama wajibi ya bi wadannan matakan da zamu kawo kamar haka:

1. Zaben Fannin da ake bukatar neman ilimi   ko kuma kwarewa a kai

Kasancewar fannonin computer suna da daman gaske, abin da mutum ya kamata ya fara yi shine, ya fara zabar fannin da yake bukatar samun kwarewa a kai. Yin haka shine abin da zaya ba mutum damar ajiye hankalinsa a waje guda, tare da koyon abin da ya kamata a cikin dan kankanen lokaci. Mutane da yawa kan bijiro da aniyarsu ta koyon ilimin computer ne a lokacin da bukatar yin hakan ta taso, ko dai saboda an bukace su da su yi hakan ne a a wajajen aiyukansu ko kuma saboda sha’awar ilimin computer da suke yi.  Akwai bangarorin ilimin computer da dama da mutum zaya iya koyo tare da samun kwarewa a kai. Wadannan bangarori sun hada da Graphic design (yanda ake gyara hotuna da videos), word document (Yanda ake rubuta ko kuma typing), Spreadsheet, Presentation, Web design, programming (Yanda kae hada applications na waya da computer), harkar kasuwanci a internet (wato Digital marketing a turance) da dai sauran dubban ilimummuka da suka shafi bangarori da dama na computer. Tabbas mutum zaya iya samun kwarewa a kan sama da abu daya da ya shafi computer, sai dai abin da ya kamata mutum yayi shine, ya tabbatar ya dauki abu daya a lokaci guda, ba ya dauki abubuwa da dama ba a lokaci guda kuma ya ce yana so ya koye su duk a lokacin, wannan baya yiyuwa! Saboda a karshe mutum zaya kasance bai samu kwarewa a kan ko daya daga cikin fannonin ba.

See also  YADDA ZAKU IYA DAWOWA DA DUK WANI MESSAGE NA WAYARKU DAYA GOGE

2.  Wajen Da mutum zaya iya neman wannan ilimi a saukake

Mafi yawancin mutanenmu a yanzu abin da suka dauka shine, dole ne sai ka je makarantar computer ka yi certificate kafin ka iya koyon ilimin computer. Wannan zance kwata-kwata ba haka yake ba! A wannan zamani na kafar sadarwa ta internet, mutum baya bukatar sai ya je makaranta kafin ya samu wani ilimi. Domin kusan duk wani abu da zaka iya nema a ilimance, to idan ka je a Internet zaka iya samun shi cikin sauki. A yayin da wasu mutanen kan bata lokutansu a internet wajen yin abubuwan da ba zasu taba amfanarsu ba (misali chatting da kuma download na abubuwan da ba zasu amfane su ba), wasu mutanen kuma sun maida internet wata makaranta ta musamman inda suke samun ilimi a kan dukkan wani abu da ya shige masu a duhu. Akwai shafukan internet da yawa da mutum zaya iya zuwa domin koyon wani ilimi na computer da ma wasu sauran ilimummuka.  Babba daga cikin wadannan shafuka shine Google. A duk lokacin da kake bukatar samun Karin bayani akan wani abu, to da zaran ka sanya wannan abin tare da nemo shi a google, zaka samu sakamako na shafuka da dama da suka yi sharhi akan wannan abin da kake neman bayani ko kuma sani a kansa.  Kasancewar wasu mutane sun fi gane abu idan suna kallon yanda ake yin shi kai tsaye, zaku iya amfani da kafar YouTube domin samun video tutorials a kan ko wane abu da mutum ke bukatar koyo. Baya ga wannan kuma, zaku iya kulla mu’amala da mutanen da kuka san suna da masaniya kan wannan fannin da kuke neman ilimi akai, domin zasu iya taimaka maku a yayin da kuke bukatar neman taimako akan wani abu da ya kakare muku. Shafin SADARWA daya ne daga cikin shafukan da zaku iya yin tambaya akan duk wani abu da ya shige muku duhu, kuma a amsa muku a cikin lokaci. A ko da yaushe zaku iya tuntubarmu domin neman Karin haske akan wani abu da baku fahimta ba ko kuma kuke neman sani a kai.

See also  Yadda ake tura Hoto, Video, Waƙa ko kuma wani file a matsayin document ta whatsapp

Baya ga google kuma, akwai website da dama da ke gabatar da kwasa-kwasai daba-daban a kan harkar computer, wasu kyauta ne, wasu kuma ana dan biyan wani abu, amma dai abin da ake biya ko kadan bai kai kudin da mutum zaya kashe a wajen halarta wata makarantar computer ba.

3. Mallakar kayan aiki

Bayan mutum ya zabi fannin da yake son ya nemi kwarewa a kai, kuma ya san wuraren da zaya je ko kuma ya shiga domin nemo wannan ilimi, abu na gaba shine ya mallaki kayan aikin da zaya iya bukata a lokacin da yake neman wannan ilimi. Misali mutumen da yake bukatar koyon Graphic design (wato yanda ake gyara hoto da video) to akalla yana bukatar ya mallaki computer da kuma graphic software kamar Photoshop  ko kuma CorelDraw.. Wanda kuma yake bukatar ya kware a kan harkar da ta shafi amfani da computer a ofisoshi ko kuma wajen kasuwanci, to shima yana bukatar mallakar computer tare da office suit ko kuma package kamar Microsoft Office, wanda shi kunshi ne da ya kan zo da duk wata software da mutum zaya iya bukata a wannan fannin kamar Word, Excel, presentation da dai sauransu. Ga wanda baya da computer kuma, zaya iya amfani da computocin makaranta, café ko kuma idan yana da wani aboki amintacce da ya mallaki computar, to zaya iya amfani da ita domin yin gwaji akan abin da yake koyo. Hasali ma, mafi yawa daga cikin wayoyin hannu na zamani da muke da su, za’a iya amfani da su wajen koyon kusan duk wani abu da mutum ke bukatar koyo. Mafi sahihancin hanya da mutum zaya auna fahimtarsa akan wani abu da ya koya shine ta hanyar aiwatar da duk abin da ya koya a aikace, ba wai kawai ya karanta ba.

See also  KO KASAN RABE-RABEN LOGO DA MUKE DASU?

Wadannan matakan sune in dai har mutum ya dauke su, to zaya iya koyon ko wane ilimi yake bukatar koya a fannin computer a saukake ba wai dole sai ya je makarantar computer ba. Kada ku manta kuma, a ko da yaushe burin shafin KARATUNTURANCI shine mu ga mutane masu hazaka suna tashi tsaye domin neman ilimi, shi ya sa a ko da yaushe, a shirye muke wajen taimakawa ga dukkan wanda ke bukatar hakan…

Allah ya daukaka Al-ummar hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button