BANBANCI TSAKANIN MTN “SME DATA” DA KUMA “DIRECT DATA”
SME DATA da DIRECT data dukkansu tsarin amfani da data ne na kamfanin MTN da suke tafiya akan fuskokin lamba guda biyu, ita DIRECT DATA tana da 131 ita kuma SME DATA tana da 461.
DIRECT DATA an samar da itane domin duk wani mutun da yake amfani da layin MTN hakanne ma yasa kowa zai iya siyan DIRECT DATA a ko wane lokaci, haka kuma ita DIRECT DATA ana siyan ta rana ‘daya (daily) ko ta sati (weekly) da kuma ta wata (monthly).
SME DATA ita kuma an samar da itane saboda kamfanunnuka ko wasu wajajen ayyuka da suke da ma’aikata domin idan zasu sayi data su rarraba ma ma’aikatansu shine zasu sayi SME DATA.
Adadin kwanakin ingancin SME DATA shine kwana 30 kuma SME DATA basu da tsarin daya gaza kwana 30 (monthly) sai dai indan mutun ya cinye kafin watan sai ya sake saye.
SME DATA tana da sauƙi fiye da DIRECT DATA kuma babu wani banbanci wajen ƙarko a tsakaninsu, sai ma dai wasu da suke hasashen cewa SME DATA tafi DIRECT DATA sauri wajen yin aiki saboda anyi tane domin kamfanunnuka akan tsarin kasuwanci, shiyasa ma suke ganin kamar tafi saurin ƙarewa wajen amfani sama da DIRECT DATA.
Zuwan wasu kamfanunnukan da suke sana’a dillancin data a tsakanin mutane, sun kawo tsarin MTN SME DATA acikin tsarinsu na dillancin data domin irin sauƙin da SME DATA take dashi, kuma sun ƙara bama duk mai sayan SME DATA damar siyanta ta hanya mai sauƙi da kuma hanyar turata cikin sauƙi.
Duk wanda yakeson ƙarin bayani ko kuma koyan yadda zai iya zamowa ‘daya daga cikin masu sana’ar dillancin data zai iya tuntu6ar Abu Ibrahim