HANYAR DA ZAKA BI KA GANE LOGO ƊIN DA KA ƙIRƙIRA IDAN AN TAƁA SAMAR DA IRIN SHI
Da wanda yake ƙirƙirar logo da wanda yake bada aiki a ƙirƙirar mashi logo duka wannan hanyar zata amfane ku.
Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen binciken ko wane irin logo ne idan an ta6a samar dashi ko kuma idan akwai wani logo wanda suke kamanceceniya dashi, amma wannan itace hanya ta farko kuma wadda take da sauƙi sosai, sauran hanyoyin suma zanyi bayaninsu nan gaba.
A matsayinka na wanda yake kasuwanci ko wata harka da take da buƙatar a samar mata da logo, yana da kyau ka samu ayi maka design na logo wanda babu wani wanda ya ta6a yin register wani abu dashi, tunda kaima zaka iya kaiwa matakin da za kayi ma naka register.
Haka kaima mai aikin..
A matsayinka na graphic designer yana da kyau kuma ya kamata ace duk logo ‘dinda za kayi ma wani design ka tabbata wani baiyi irinshi ba har akayi register dashi, domin logo abune mai matuƙar muhimmanci.
Mafi yawan lokuta ana samun daidaito na wani logo da wani logo wajen ƙirƙira, ba zasu zamo kama iri ‘daya komai da komai ba, amma zasu iyayin kamanceceniya ta wata fuskar.
Duk logo wanda zai zamana ana saka ran za’a kai wani mataki babba ana amfani dashi to akwai buƙatar a tantanceshi kafin fara amfani dashi.
‘Daya daga cikin hanyoyin itace nayi bayaninta a hoton da yake tattare da wannan post ‘din mai dauke da matakai guda shida (6)
1- Na farko za’a shiga cikin browser ta google chrome, aje inda wasu 3dots suke.
2- Za’a maida tsarin wayar zuwa na computer desktop idan a waya ne kenan, mai amfani da computer kuma kai tsaye zai wuce mataki na gaba, ba tare da yayi hakan ba shi.
3- Daga nan sai a duba inda aka rubuta image sai a shiga wajen.
4- Mataki na hudu shine za’aga hoton camera ya fito a wajen (search bar) sai a shiga wajen da hoton camera ‘din ya fito.
5- Za’aga za6i guda biyu…
*Paste image URL
*Upload an image
….sai a shiga za6in na biyu wanda aka saka upload an image.
6- Mataki na shiga shine zai bada dama a ‘daura hoton logo ‘dinda akeso a tantance idan aka danna wajen choose file.
Tabbas idan dai mutun yabi yadda na nuna a jikin wannan hoton da kuma wannan bayanin da nayi har ya samu ya daura hoton logo ‘din da yake son tantancewa babu shakka zai samu abunda yake buƙata.
Ku jaraba hakan da wani logo dan ya zama gwaji, ta yadda koda zuwa watarana ba zaku manta ba.
Akwai wasu website da suma ake irin wannan binciken dasu, sune:
http://Tineye.com
Idan akabi suma wa’dannan za’a samu abunda akeso.
Abu Ibrahim