Tambayoyi a Musulunci

ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?Tambaya:
Salam. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?

Amsa:
To dan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.
Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za’a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa
28/11/2015

See also  IDAN DIREBA YA KASHE MUTANE BAKWAI, YAYA KAFFARARSA?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button