Addu'o'iTambayoyi a Musulunci

KARANTA ADDU’AR BUƊE SALLAH (DU’A’UL ISTIFTAHI)


????????????????????????????❓
:
Assalamu alaikum, yayana ina godiya mara adadi, dan Allah ina so a dan kara min bayani a kan addu’o’in da ake yi kafin a ta da sallah.
:
????????????????❗️
:
Wa’alaikumus salám, Sahabbai da dama sun ruwaito cewa Annabi ﷺ ya kasance yana buɗe sallah da addu’o’i da dama da suka haɗa da:

  1. Abu Hurairata Allah ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin shiru a tsakanin kabbarar harama da karatu na ɗan lokaci, sai na ce ya Manzon Allah Mahifina da Mahaifiyata fansa ne a gare ka, yin shiru ɗin da kake yi a tsakanin kabbara da karatu mene kake faɗi? Sai Manzon Allah ya ce: Ina cewa ne:

“اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ ، كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنَ الخَطَايَا ، كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ ، اللَّهُمَّ اغْسِلْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ ، وَالثَّلْجِ ، وَالبَرَدِ”.

Bukhariy (744), Muslim (598).

  1. Nana A’isha Allah ya qara mata yarda ta ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya kasance idan zai buɗe sallah yana cewa:

“سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ وَتَعَالَى جَدُّكَ ، وَلَا إِلَهَ غَيْرَكَ”.

Abu Dáwud (776), Attirmizhiy (243).

  1. Daga Aliyu Allah ya qara masa yarda ya ce: Ya kasance Manzon Allah ﷺ idan ya miqe zai yi sallah yana cewa:

“وَجَّهْتُ وَجْهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ حَنِيفًا ، وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ ، إِنَّ صَلَاتِي ، وَنُسُكِي ، وَمَحْيَايَ ، وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ ، لَا شَرِيكَ لَهُ ، وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِمِينَ ، اللهُمَّ أَنْتَ الْمَلِكُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْتَ رَبِّي ، وَأَنَا عَبْدُكَ ، ظَلَمْتُ نَفْسِي ، وَاعْتَرَفْتُ بِذَنْبِي، فَاغْفِرْ لِي ذُنُوبِي جَمِيعًا ، إِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ ، وَاهْدِنِي لِأَحْسَنِ الْأَخْلَاقِ لَا يَهْدِي لِأَحْسَنِهَا إِلَّا أَنْتَ ، وَاصْرِفْ عَنِّي سَيِّئَهَا لَا يَصْرِفُ عَنِّي سَيِّئَهَا إِلَّا أَنْتَ ، لَبَّيْكَ وَسَعْدَيْكَ وَالْخَيْرُ كُلُّهُ فِي يَدَيْكَ ، وَالشَّرُّ لَيْسَ إِلَيْكَ ، أَنَا بِكَ وَإِلَيْكَ ، تَبَارَكْتَ وَتَعَالَيْتَ ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ”.

See also  JANABAR GWAURAYE A LOKACIN SANYI

Muslim (771), Annasá’iy (897).

Asshaikh Abdul’aziz bn Baaz ya ce: “Wannan addu’ar ta uku Annabi ﷺ ya kasance yana karanta ta ne a sallar nafila ta dare, amma a sallar farillah, abin da ya fi shi ne karanta waccan addu’ar ta farko ko ta biyu, wannan shi ne abin da aka kiyaye daga gare shi ﷺ a sallar farillah, amma buɗe sallah da addu’a mai tsawo ya kasance yana yin ta ne a sallar tahajjud”.
Duba Fataawá Nurun Alad Darb (8/182).

Baya ga waɗannan akwai wasu addu’o’in da dama da Manzon Allah ﷺ yakan buɗe sallarsa da su da ba zai yiwu a kawo su duka a nan ba.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button