Ɗaurin Shekara 3 ne hukuncin duk wanda ya doki Matar shi
Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah
Dukar mata wata baƙar ɗabi’a ce ta zalunci da cutarwa da mazaje suke yiwa matan su a wannan zamanin, shiyasa Manzon Allah (SAW) yace: “Yanzu ɗayan ku ko kunya baya ji ya gama dukar matar shi da rana kamar wata baiwa sannan kuma da dare ya lallaɓo yazo wurin ta yana mata daɗin baki (wai yana so yayi jima’i da ita)” Au kama Qala.
Hakan ne ma yasa Sarkin Haɗaɗɗiyar Daular Kano Na 14, Malam Muhammadu Sanusi II yace: duk matar da Mijin ta ya dake ta to ta rama !
Anyway, Majalisar tarayya tayi doka inda ta haramta Miji ya doki Matar shi, ko mace ta doki mijin ta, kai ko zungurin ta kayi da yatsa to ka aikata laifi kuma zaka fuskanci hukuncin ɗauri a gidan gyaran hali har na tsawon Shekaru 3 tare da biyan tarar kuɗi ₦200,000.00 kamar yadda Sashi na 19 (1) dana 46 da 48 na Violence against Persons Prohibition act, 2015 ya bayyana.
Shi kuma Sakin layi na biyu na Sashi na 19 ɗin cewa yayi koda Niyyar dukar ta kayi, ko niyyar zungurin ta da yatsa to ka aikata laifin da za’a ɗaure ka har na tsawon Shekara ɗaya ko kuma tarar kuɗi ₦100,000.00 ko kuma duka biyun.
Haka Shima sakin layi na 3 cewa yayi duk wanda ya bada Shawara akan a doki Mace ko a zungureta da yatsa ko irin a murɗe mata hannu ɗinnan to ya aikata laifi, Hukuncin sa shine ɗauri a gidan gyaran hali na tsawon Shekara ɗaya, ko tarar kuɗi ₦200,000.00 ko kuma duka biyun.
Haka sakin layi na 4 ya ƙara da cewa kai duk wanda ya taimaka aka doki mace, ko aka zungureta da yatsa ko makamancin haka, to ya aikata laifi shima, Hukuncin sa Shine tarar kuɗi ₦200,000.00 ko kuma zama gidan gyaran hali na tsawon Shekara ɗaya.
Saidai wannan dokar tana aiki ne ga mutanen dake zaune a Abuja kawai kamar yadda Sashi na 47 na Violence against Persons Prohibition act, 2015 ya faɗa, amma akwai jihohi da suka fara yin adopting wannan dokar, dan haka muna fata sauran Jihohin suma suyi.