TechWhatsApp

Yadda ake magance matsalar WHATSAPP BACK DATEKa ta’ba fuskantar matsalar whatsapp update? Kuma ka kasa samun damar yin update ‘dinshi kasantuwar GB ne kake amfani dashi ko kuma wani whatsapp ne dai wanda babushi a playstore, ko kuma baka da halin isassar data wadda zatayi maka update ‘dinshi a daidai lokacin, kuma gashi kana da wani important record da kakeso ka fitar ko kuma ka dauka gashi kuma whatsapp ‘din yayi expire ya’ki ya bu’de bare ma ka samu damar shiga cikinshi.

Ka natsu ka karanta nasan zaka fahimta kuma zaka amfana.

Whatsapp application yana amfani da information ‘din da wayarka take bashi ne yana sanin halin da wayarka take ciki harma yasan mene ya kamata yayi, kamar yadda kaima kake amfani da wasu abubuwan dan kasan mene yakamata kayi a lokacin.

-Misali
Kana duba lokaci (time) ko kwanan wata (date) dan kasan a wane lokaci kake kuma mene ya kamata kayi a lokacin, to kamar hakane shima manhajar whatsapp yake yi kuma a haka aka tsarashi.

Idan manhajar whatsapp ‘dinda yake a saman wayarka kayi download ‘dinshi ne tun watan August ne sannan kuma anyi shi ne a farkon watan August kuma an tsarashi da yayi expire a ‘karshen watan November, taya kake tunanin zai iya sanin lokacin expire ‘dinshi yayi idan ba tare da wayarka ta sanar dashi ba? To tabbas hakane wayarka itace take sanar dashi.

Tsaya ka natsu kaji…
Idan irin hakan ta faru dakai ga hanyar da zaka magance ta a lokacin dan ka biya bu’katarka kafin ka samu mafita ta musamman.

1- Zaka rufe data ‘dinka.
2- Zaka tafi cikin settings na kan wayarka.
3- Acikin settings zaka shiga Apps
4- Zaka nemo whatsapp aciki, sai ka shiga cikinshi
5- Zaka ga inda aka rubuta UNINSTALL da FORCE STOP sai ka danna na biyun wato FORCE STOP ‘din.
6- Daga nan sai ka fito daga wajen kA tafi wajen settings na Date & Time ‘dinka, ka shiga ciki.
7- Farko zaka fara cire Automatic Date & Time ya zama ba’a automatic yake ba.
8- Na biyu zaka shiga wajen Date Setting ‘din ka mai dashi August, ma’ana dai lokacin da whatsapp ‘dinka yake lafiya kafin yayi expire kenan.
9- Daga nan sai ka fito daga cikin settings ‘din duka.
10- Kawai kaje ka bude data ‘dinka ka shiga cikin whatsapp ‘dinka kai tsaye, zaka ga ya dawo lafiya lau kuma yana aiki kamar bai ta’ba expire ba.

Zaka iya cigaba da aiki dashi har sai ranar da wannan kwanan watan ya ‘kara kaiwa inda aka tsara ma whatsapp ‘dinka da yayi expire, haka kuma zaka iya ta ‘kara dawowa dashi baya duk lokacin da kaso ba tare da wata damuwa ba ko matsala.

Masha Allah
Ina ro’konka da idan har ka koyi wannan abun dana koya maka kuma har ka iya, dan Allah kaima ka koya ma wani ko wasu.

✍???? Abu Ibrahim

See also  YADDA ZAKA IYA SANIN LAST SEEN NA WANI A WHATSAPP KODA YA RUFE LAST SEEN NASHI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button