Tarihin Sayyada Fatima ƴar Annabi Muhammad (SAW)

TARIHIN SAYYADA FATIMA (AS) فَاطِمَة ٱبْنَت مُحَمَّد KASHI NA DAYA ( 1 )



Fāṭima bint Muḥammad, wacce aka fi sani da Fāṭima al-Zahraʾ, diyar AnnabinMuhammad Sallallahu Alaihi Wasallama Ce da matarsa Khadija ( RA) Mijin Fatima shi ne Sayyadina Ali ( RA) na hudu a cikin Khalifofin Rashidun ‘Ya’yan Fatima su ne Hasan da Husaini Imamai na biyu da na uku.

An haifi Sayyida Fatima (AS) a Makka, ranar Juma’a 20 ga watan Jimada Sani, wanda Yayi Dai-dai Da 15 Ga Watan Disamba 605 miladiyya Shekara ta biyar, bayan aiko wa ANNABI S.A.W da Annabci.

Malaman Ahlus Sunna sun tafi a kan cewa shekara biyar gabanin aiko ANNABI S.A.W ne aka haife ta. .
.
Sunan Mahaifiyarta, kamar yadda aka sani, Khadijah (AS).
.
Tana da shekara biyar Allah (S.W.T) ya yi wa Mahaifiyarta rasuwa.
.
Har ila yau a wannan shekarar ce Allah (S.W.T) yayiwa Abu dalib (RA) rasuwa.
.
Ya zo a kan cewa tsakanin rasuwar Khadija da Abu dalib (RA) kwana uku ne.
.
Shiya sa shekarar aka yi mata lakabi da shekarar bakin ciki.
.
Bayan rasuwarsu ne ANNABI S.A.W ya tafi da’ifa domin isar da sako

A wata Riwaya Kuma An Haifi Sayyida Fatima al-Zahra (AS):

An haifi Fatima al-Zahra (AS) ne a ranar juma’a, Ashirin ga watan Jimada Sani, shekaru biyar bayan aiko Annabi. Bayan haihuwar Manzon Allah (S.A.W) ya amshi ‘yarsa da farin ciki da amincewa, ya kuma sa mata suna Fatima.
.
An haifeta kuma ta tashi a gidan Annabci, ta tarbiyyantu a inuwar wahayi, ta kuma sha kaunar imani da kyawawan dabi’u daga Khadija.

Nasabarta Nana Fadima ( R.A ). Bayyanen nan lamari ne domin kuwa duk wanda yasan tarihin mahaifinta da nasabarsa to ya san nasabarta domin kuwa ita ‘Yarsa ce jini da tsoka.
.
Nasabarta awajen mahaifinta.
Nana Fadima
‘Yar Muhammad Rasulallahi dan
Abdullahi dan
Abdul Mudallib dan
Hashim dan
Abdul-Munafi dan
kusayyi dan
kilabin dan
Murarata.

Daga nan Nasabarta ta zarce har kan Adnan daga nan kuma har zuwa kan Annabi Ibrahim ( AS).

Nasabarta ta wajen mahaifiyarta kamar yadda aka san Abban Nana Fadima sune asalin Larabawa, kuma cikakkun kuraishawa, to haka Nana Khadija mahaifiyar Nana Fadima domin kakannin su daya.

Ga nasabarta ta wajen mahaifiyarta. Nana Fadima

‘Yar Nana khadija ce
‘Yar khuwailadin dan
Asadin dan
Abdul’Uzza dan
Kusaiyin dan
Kilabin dan
Marrata.

Nasabar Manzon Allah (S.A.W) ta hadu da ta Nana Khadija tun akan kakansa na hudu wato kusaiyi. Wannan ita ce Nasabar Nana Fadima a takaice.

Fatima ta kasance mai dauke da ruhin ANNABI (S.A.W) da dabi’unsa, don haka ta zama mai gado da kuma tsananin kama da shi, har ma A’isha ( RA) ta taba cewa:

“Ban ga wanda ya fi kama da Manzon Allah (S.A.W) a rashin magana da kyauta fiye da Fatima ‘yar Manzon Allah ba, a tsayuwarta da zamanta.

Ta kasance idan ta shiga wajen Annabi (S.A.W) ya kan mike ya tarbe ta, ya zaunar da ita a wurin zamansa.

Haka nan idan Annabi ya shiga gare ta, ta kan mike daga wajen zamanta ta tarbe shi, ta zaunar da shi a wajen zamanta.

Allah Ya so Fatima ta fara yarintarta a wani yanayi mafi tsananin wahala da kuntatawa daga matakan da’awar Musulunci; kuma wanda mahaifanta suka fi shan wahala da cutuwa a cikinsa.

Ga dai Kuraishawa nan na tilasta takunkumi tattalin arziki a kan ANNABI (S.A.W) da danginsa daga banu Hashim da mayar da su saniyar-ware.

A wannan lokacin ne aka tsare ANNABI (S.A.W) a Shi’abi Abi Talib tare da matarsa Khadija, ‘yarsa Fatima da sauran musulmi.

Shekarun takunkumi sun wuce tare da matsanancin hali, har zuwa lokacin da ANNABI (S.A.W) ya fita daga cikinsa tare da wadanda ke tare da shi alhali Allah Ya rubuta masa nasara da galaba.

Khadija kuwa ta fita daga cikin shi alhali shekarun sun yi mata nauyi, gajiyar takunkumi da matsalolinsa sun raunana ta. Wannan ya sa ajalinta ya gabato.

Allah Ya zabar mata makwabtakar Sa, inda ta rasu a wannan shekara, bayan ‘yan watanni kuma sai Abu Dalib baffan ANNABI (S.A.W) mai kariya da taimakon Musulunci; wanda ANNABI (S.A.W) ya bayyana yadda ya yi rashinsa da fadarsa cewa: “Kuraishawa ba su fara matsamin ba har sai da Abu Dalib ya yi wafati ya rasu.

Hakika ANNABI (S.A.W) ya yi bakin ciki kuma ya ji kadaici a saboda rabuwa da Khadija. Domin ya yi rashin Khadija matarsa, masoyiyarsa kuma mai taimakonsa. Kamar yadda ya yi rashin baffansa mai kariya gare shi; don haka ya kira wannan shekara da sunan Shekarar Bakin-Ciki.

Fatima, karamar ‘yar Manzo (a wannan lokaci) ma ta rayu cikin wani bangare na wannan bakin ciki, ita ma ta yi makoki, don kuwa ita ma bala’in wannan shekarar ya taba ta; yayin da ta rasa uwa mai tausayi; alhali kafin nan ta koshi da kaunarta da lurarta, don haka (yanzu) ta lullubu da bakin-ciki da maraici.

Sanannen abu ne cewa dole ne wannan rasuwa ta girgiza Fatima don kuwa ta rasa mahaifiyarta, ta rabu da cibiyar kaunarta, don haka sai dacin rabuwa ya cika zuciyarta ya kuma girgiza ta.

Babanta ANNABI (S.A.W) ya dandana bakin-cikin Fatima; yayin da ya ga karamar ‘yarsa na zubar da hawayen rabuwa, sai zuciyarsa mai tausayi ta yi kuna, jiyayyar nan tasa ta uba mai kauna ta gaskiya ta tabu, don haka sai ya kusanci Fatima don ya musanya mata abin da ta yi rashi na kauna da kusanci da kaunarsa da taushin zuciyarsa.
.
Hakika ANNABI (S.A.W) ya so Fatima kuma ita ma ta so shi; ya tausaya mata kuma ita ma ta tausaya masa.

Babu wanda ya fi Fatima kusa da shi kuma ba wanda yake so kamar ta. Ya sha jaddada wannan alaka a cikin hadisansa yana bayyana matsayinta a cikin al’ummarsa. Ga kadan daga cikin abubuwan da ya fadi dangane da ita:

“Fatima wani yanki ne daga gare ni, wanda ya fusata ta ya fusata ni”. da kuma cewa:
.
“Lallai Fatima wani yanki ne daga gare ni, (duk) abin da ke cutar da ita yana cutar da ni” A wani wajen kuma ya ce:
.
“Ya Fatima, ashe ba ki yarda da kasancewa shugabar matan duniya ba, kuma shugabar wannan al’umma da shugabar matan Muminai”.

Fatima na girma alhali kaunar babanta gare ta na girma tare da ita, tausayinsa a kanta na karuwa; kuma ita ma tana musanya masa wannan kauna, tana cika zuciyarsa da lura; don haka ya kira ta da Ummu Abiha (wato uwa a wajen babanta)”..

Ta kasance tana ji da shi da tausaya masa irin tausayin uwa ga ‘ya’yanta, tana kuma lura da shi kamar yadda uwaye mata ke lura da ‘ya’yansu kanana, wanda hakan ya zamanto abin koyi ne na tsarkakkar alakar uba (da ‘ya’yansa) wajen gina ‘ya’ya da fuskantar da dabi’u da rayuwarsu, da cika zukatansu da kauna da tausayi. Hakika wannan alaka ta zama babbar abar misali a fagen renon ‘ya mace a Musulunci da lura da ita, girmama ta da daukaka matsayinta.

Allah (S.W.T) ya yi wa Sayyidah Zahra baiwa da karamomin da ba za su kirgu ba. Tun asali ta zama fansa ga Mahaifinta daga gorin da mushirikai suke masa na ganin sa a matsayin mai yankakken baya. Shi ne Allah (SWT) ya ba shi Fatima (AS) kamar yadda ya zo a Suratul Kauthar. Sannan Sayyidah Zahra ta zama tsarkakakken tsatso daga tataccen ruwan tuffah daga Aljanna, ta yadda har ma Manzon Allah (SAW) yana cewa idan ya so ya ji kamshin Aljanna yakan sumbaci Fatima ne.

Kana ga shaidar sauki da rashin fargaba da zullumi da Nana Khadija ta bayar wajen daukar cikin Fatima (AS). Sannan ga magana da hira da ta gudana tsakaninta da Sayyidah Zahra tun tana ciki, kamar yadda ya zo a littafin Imamu Shafi’i da Dahlawiy. Kana ga mataye hudun da suka zo daga Aljanna don taya ta hidimar haihuwarta, inda ta zo duniya tana mai sujada ga Allah (SWT) tana mai daga yatsunta zuwa sama. Manzo ya yi farin ciki da wannan abar haihuwa, ya sa mata suna Fatima bisa wahayi daga Allah (SWT).

Cikin ikon Allah Sayyidah Zahra ta rika girma da gama-garin yara ke yi a wata ruwayar cikin sati daya. baya ga wannan suna tana da sunaye da yawa saboda girmanta da kuma daukakarta, kamar yadda ake cewa; “yawan sunaye na nuni ga girman mai su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button