RamadanTambayoyi a Musulunci
NA CI ABINCI BAYAN ALFIJIR YA KETO
Tambaya:
Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe Alfijir ya keto tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu?
Amsa:
To Malam, mutukar ba da saninka kayi haka ba, to Azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai Azumi yayi kokwanton hudowar Alfijir, to ya halatta a gare shi yaci abinci, saboda wanzuwar dare shine asali, kamar yadda Ibnu-Abbas yake cewa: “Allah ya halatta mana cin abinci – a Ramadhana – mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir”, saidai in da zai yi kokwanton faɗuwar rana to bai halatta a gare shi yaci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shine asali.
_Allah ne mafi sani._
20/07/2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.