RamadanTambayoyi a Musulunci

MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA



Tambaya:
Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai naji mijina ya danne ni, nayi ta ƙoƙarin na kwace amma sai yaci ƙarfina ya sadu da ni, alhalin muna Azumi, don Allah Malam a taimaka min da mafita. Allah ya sanyawa zuriyarka albarka.

Amsa:
Ƴar uwa, mutukar yadda kika sffanta haka abin ya faru, to babu kaffara a kan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah, amma shi kuwa ya saɓawa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadhana, kuma dole yayi kaffara, ta hanyar ƴanta kuyanga, in bai samu ba sai yayi Azumi sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da Miskinai sittin, kamar yadda yazo a Hadisin Bukhari mai lamba ta: (616).

Allah ne mafi sani.
15/07/2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button