Tambayoyi a Musulunci

HUKUNCIN KASHE KWADI DA CIN NAMANSU



Tambaya:
_Assalamu alaikum malam, menene ingancin hadisin dayake cewa “Manzon Allah S.A.W. ya hana kashe kwadi saboda kukansu tasbihi ne ga Allah”?_

Amsa:
Wa alkm slm, Tabbas ya tabbata a hadisin Abu-Dawud mai lamba (5269) da kuma Nisa’i (2/202) cewa: wani likita ya tambayi Annabi S.A.W. akan kashe kwadi saboda sanyawa a magani sai Annabi yahanashi kashesu”, Baihaki ya ruwaito daga maganar Abdullahi bn Amr bn Al-Ass cewa, ” kada kukashe kwadi saboda kukansu tasbeehi ne ga Ubangijinsu”. duk da cewa hadisin zai iya daukar cewa yaji ne daga Manzon Allah (S.A.W) saidai Hafiz bn Hajar yana cewa “Abdullahi bn Amr bn Al-Ass ya shahara da yin riwaya daga malaman yahudu da nasara don haka ba dole ne yazama daga Annabi yaji ba”.

kashe kwadi haramun ne saboda hadisin Abu-dawud da Nisa’i wanda yagabata, kamar yadda cin su yake haramun ne, saboda bazai yiwu a ci dabba ba sai bayan ranta ya fita.

Allah ne mafi sani.
11/11/2018

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  ZAN IYA DORA RIBA, IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button