Zanyi wannan bayani amma badan kaje ko kije ki kulle wa wani account dinsa ba dan Allah
Zanyi shi ne domin kasan matakan da masu kutse (Hackers) sukebi wajen Hacking din Account dinka na Facebook, kaga qila daganan kaima sai ka nemi matakin kariya daga wajensu..
Wato abinda na lura dashi sosai a yanzu shine ana yawan kullewa mutane account dinsu na shafin “Facebook” (Facebook Hack) wanda yawanci Hausawanmu ne akeyi wa wannan iskanci..
To shiyasa nace zanfada maku matakan da hackers sukebi wajen hacking din account din mutane qila hakan ta taimaka maka wajen kulawa sosai..
Kafin na tafi kai tsaye ya kamata kasan “Hackers” din ma sun kasu kashi-kashi, amma wadanda akafi sani aciki kuma sukayi fice sune:
1. Grey hat hackers
2. White hat hackers
3. Black hat hackers
Wato akwai dabaru gida biyu zuwa ukku da hackers suke amfani dasu wajen kullewa mutane Facebook dinsu ma’ana (Hacking).
Wadannan dabaru sune kamar haka:
1. Hasashen “Password Guessing” da kuma “Social Engineering”.
Da kuma ta hanyar yaudara.
” Password Guessing: Wato yanzu da yawan hackers sun gano cewa mutane da dama suna amfani da numbers din wayarsu, shekarun haihuwarsu, da kuma sunayensu wajen sanya password dinsu na Facebook.
Wannan shine yabaiwa Hackers babbar dama wadda a duk lokacin da suka buqaci kwace maka account sai suyi hasashen amfani da number wayarka kokuma sunanka da sauransu.
Domin kauce wa irin wannan hadari sai ka kiyayi sanya Password dinka da yakeda sauqi ko yake da alaqa da number ka ko sunanka.
“Social Engineering: Wato hanya ce mai zaman kanta wadda Hackers suke amfani da ita domin suyi hacking din Computer dinka kokuma account dinka, ita ake kira da ” Zamba Cikin Aminci” wato zasuyi amfani da kusanci dake tsakaninku kai kana ganin kayarda da mutum bari kabude password dinka a gabanshi sai shi kuma ya kyalla ido a lokacin da kake sanya password din account dinka, shi ake kira da (eaves dropping) da zaran yaga me ka rubuta shikenan sai yayi amfani dashi ta hanyar (Password Recovery) kokuma ta hanyar yin Installing wani Application wacce zatadinga yin leken asiri ne tareda tura bayanai zuwa wurin hacker din.
3. Yaudara: Shi kuma wannan mutum zai karbi number wayarka ne sai yaje yasanya yayi “Password Recovery” daganan zasu turo maka wani Code a wayarka sai shikuma Hacker din sai yayi sauri yakiraka ta waya yace maka dan Allah anturo maka wani Code? Idan kace: “Eh” sai yace to dan turominsu ina jaraba cike wani File ne kokuma wata rigister kokuma samun wani Bonus da dai sauransu domin ya yaudareka, kaikuma idan katura shikenan zaiyi Hacking account din yadinga amfani dashi kokuma yayi abinda yakeso yayi dashi..
Inafatan kowa ya fahimta kuma fatan babu wanda zai dauki wannan hanyar dan cutar da wani
Whatssp only: 08137350232