Graphic designTech

MUHIMMANCIN ILIMIN GRAPHIC DESIGN



Babu wani ilimi ko sana’a wand yakai Graphic Design chu’danya cikin fannonin al’amura na rayuwar yau da kullum.

Idan za muyi duba akan al’amuran da muke gudanarwa na rayuwa tun daga kan ilimin da muke nema har ya zuwa kan kasuwancinmu da sana’o’inmu da al’adunmu baki ‘daya zamu hangi ayyukan graphic design a ciki tsundun, uwa uba kuma mu hangi 6angaren siyasa, anan kuma zamu ga cewa gudunmuwar da graphic design yake badawa acikin fannin shine kaso mafi rijaye.

Tunda har muka hangi cewa aikin graphic design ya shiga cikin ko wace irin hul’da ta rayuwarmu, to hakan zai sa mu fahimci irin damar da graphic designers suke da ita, ta samun aiki a ko’ina kuma ta ko wane irin 6angare.

Fahimtar irin damar da graphic designers suka samu shine matakin farko da zai iya jagorantarmu wajen jin muna so mu koyi ilimin graphic design, ko kuma yaranmu su koya, duk dan damu dasu kowa ya samu irin wannan damar da graphic designers suka samu.

A matsayinka na ‘dan makaranta wanda yake karatu a makarantar secondary ko ta gaba da secondary, neman ilimin graphic design bazai zame maka cikas ba wajen hanaka yin karatunka da kake yi madamar ka san irin tsarin da zaka tafiyar da neman ilimin naka na graphic design.

Haka kaima da kake aikin government ko kake kasuwanci ko wata sana’a ta hannu, babu wata tangar’da da neman ilimin graphic design zai kawo maka da zata hanaka samun damar cigaba da gudanar da ayyukanka kamar yadda ka saba yi.

Matan aure da ‘yan mata suma haka, suna da dama sosai da isasshen lokaci wanda zasu iya sadaukar dashi domin neman ilimin graphic design.

Ilimin graphic design shine yake ba ma wanda yake koyanshi damar samun ku’din kashewa tun kafin ya ‘kware a fannin, dan akwai da yawa daga cikin wa’danda na koya ma graphic design, tun banyi nisa wajen koyar dasu ba suke gaya mun sunyi aiki an biyasu. Haka kuma shine aikin da baya bu’katar sai ka ha’du da wanda za kayi ma aikin kunga juna ido da ido, wanda wannan damar tafi bada tsari mai kyau a wajen matanmu na arewa wato musulmai wanda idan suka iya aikin graphic design ba dole sai sunyi chu’danya da mazajen da ba muharramansu ba wajen gudanar da aikinsu.

Kamar yadda kullum ake bude sabbin kasuwanci da kamfanoni a ko wane 6angare na duniya haka graphic designers suke ta ‘kara samun damar guraben ayyuka a wajaje daban-daban harma sunyi ‘karanci akan yadda ake bu’katarsu.

Mafi yawan mutane suna da ra’ayi tare da bu’katar koyan ilimin graphic design amma rashin damar mallakar computer da basu dashi ya hanasu yun’kurin neman ilimin graphic design. Idan kana daga cikin irinsu tsaya kaji…

Cigaban da duniya take samu a 6angaren ilimin technology akwai gudunmuwa babba wadda graphic designers suke badawa ta ‘bangarori bila’adadin, hakan yasa aka samar da wasu manhajoji na wayar Android (Android Applications) wa’danda graphic designers zasu iya yin ko wane irin ayyukansu dasu, kuma a ko a’ina suke.

Samun wani ilimi wanda zaka iya yin aikinshi a cikin wayarka ta hannu har a biyaka ku’din aikinka a wannan zamanin ba ‘karamin nasara bace, duba da irin halin da al’umma suka shiga na razanin tafiye-tafiye saboda halin rashin tsaro da muke a ciki da kuma birkicewar da duniyar tayi baki ‘daya, Allah ya kyauta.

Lallai neman ilimin graphic design ya kamaci al’ummar yankinmu na arewa tun daga kan yara ‘kanana harya zuwa manya, maza da mata.

Idan kana kasuwanci ko wani aikin hannu indai ka garwaya ko kika garwaya da ilimin graphic design zaka/zaki ga banbanci sosai tsakaninka da wa’danda basa da ilimin graphic design tun daga kan irin yadda zaka dunga tsara ma kanka flyers na tallace-tallace wanda basai ka nemi wani ya maka ba, ka biyashi.

Haka idan ka kasance ko kin kasance cikin masu sha’awar gudanar da ayyukan da suka shafi siyasa nanma idan kana da ilimin graphic design tabbas zaka zama wani babba a fannin.

A kullum darajar ilimin graphic design tana ‘kara hauhawa ne a duniya haka kuma al’amuranmu na yau da kullum suna ‘kara cigaba da neman tallafin ha’din gwuiwa da graphic designers kasantuwar yadda komai yake neman ya koma Digital.

Masu ilimin graphic design ya kamata su maida hankali wajen inganta iliminsu na graphic design mussaman ta hanyar da zasu iya yinshi a cikin wayarsu ta hannu a duk inda suke. Haka suma wa’danda basa da ilimin graphic design ina mai baku shawara da jefa kanku cikin layin masu koyan graphic design domin samun wasu damammaki a rayuwa.

Da dama daga cikin mutane har yanzu basu tabbatar anayin graphic design da wayar hannu ba har ya inganta, saboda sun ganin abun kamar yana da wuya ace anyi, to tabbas anayi dan ni kaina na koya ma mutanen da basan yawansu ba, kuma a halin yanzu haka suna cin moriyar graphic design da sukeyi da wayarsu ta hannu.

Akwai tsare-tsare da dama dana tanadar ma wa’danda nake koyama graphic design da wayar hannu a online ta yadda zasu koya cikin sauki, kuma Alhamdulillah suna gamsuwa sosai da hakan.

Masu tambayoyi akan ilimin graphic design da yadda ake yinshi da wayar hannu, dama wa’danda suke da sha’awar koya zasu iya tuntu’bata ako wane lokaci, insha Allah zanma mutun bayani daidai sanina.

✍???? Abu Ibrahim

See also  BANBANCI TSAKANIN MTN "SME DATA" DA KUMA "DIRECT DATA"

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button