TechWhatsApp

Yadda zaka iya karanta sakon da aka turo maka ta whatsapp kuma aka goge

Kanason ka koyi yadda zaka iya karanta saƙon da aka turo maka ta whatsapp kuma aka goge? Biyo mu kaji yadda abun yake…….

Samun damar karanta saƙon da aka goge yana da matuƙar amfani, domin idan da baya da wani amfani ga al’umma bazan yi wannan rubutunba.

Rayuwar mutanen yanzu ta sauya ba kamar yadda mutanen da sukayi tasu ba.

Amana tayi wuya, rashin gaskiya da mugunta sun yawaita, basai nayi wani dogon bayani ba kowa ya gane inda na dosa.

Da farko dai idan kanason gani duk wani saƙo wanda aka turo maka ta whatsapp kafin nan kuma aka gogeshi, abunda zakayi shine….

Kaje cikin playstore dinka kayi searching na wannan app din (ANTIDELETE) zaka ganshi yana da hoton kwandan shara a jikinshi. Bayan ka saukeshi a wayarka zaiyi verifying na whatsapp dinka da zaran ka budeshi.

Akwai wajen setting daga hannun dama, idan ka shiga akwai notification alerts wanda zaka iya saitashi akan duk wanda ya goge wani saƙon daya tura maka ta whatsapp to app din antidelete zai gaya maka, kuma da zaran ka shiga cikinshi zai nuna maka duk wani saƙo da wani ya turo maka da wanda kaima ka tura da wanda aka goge dama wanda ba’a goge ba.

Abu Ibrahim

See also  BANBANCI TSAKANIN MTN "SME DATA" DA KUMA "DIRECT DATA"

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button