HUKUNCIN AIKIN JARIDA GA MATAR AURE
Tambaya:
Assalamu alaikum. Ina yiwa malam fatan alkhairi. Don Allah malam wata tambaya na zo da ita !, Ina hukuncin aikin jarida ga matar aure ??
Amsa:
Wa alaikum assalamTo dan’uwa Allah madaukakin sarki ya umarci matar aure da ta zauna a gidanta, kada ta fita sai in tana da wata bukata mai muhimmanci, kamar yadda aya ta : 33 a suratul Ahzab take nuni zuwa hakan.
Aikin jarida aiki ne da yake bukatar cakuduwa tsakanin maza da mata, saboda mai aikin jarida za ta iya zama mai dauko rahoto, wanda dauko rahoto yana lazimta haduwa da maza, kamar yadda za ta iya haduwa da wanda ba muharraminta ba, wajan hada wani shiri da za ta gabatar, wanda hakan zai iya kaiwa zuwa barna, domin duk lokacin da mace take kadaita da namiji to Shaidan zai iya shiga tsakaninsu.
Lalura tana iya halatta abin da yake haramun, saidai anan wurin babu lalurar saboda za ta iya samun wani aikin na daban wanda za ta tallafawa rayurwarta da shi, sannan maza za su iya gamsarwa wajan aikin jarida, ta yadda zai zama, ko da mata ba su shiga ba, aikin zai ta fi daidai.
Aikin Jarida a gidan talabishin hanya ce da wani zai iya ganin matar aure ya yi sha’awarta, saboda duk wacce take gabatar da shirye-shirye dole ta yi kwalliya, wanda hakan zai iya kaiwa zuwa barna, ka ga sai ya zama haramun.
Malamai suna cewa : Duk lokacin da aka samu aikin jarida mai tsafta wanda bai sabawa ka’idojin sharia ba, to ya hallata mace ta yi, saboda duk hukuncin da aka haramta shi saboda wata illa, yana zama halal idan ta gushe, saidai da kamar wuya a samu hakan a irin kasashen da ba’a aiki da shari’ar musulunci, wannan yasa barin aikin ga mace shi ne daidai, musamman na talabishin wanda ya kunshi barna mafi gima, kamar yadda bayani ya gabata.
Allah ne mafi sani
Don neman Karin bayani duba : Al-mar’atu Almuslima Almu’asirah na Ahmad Ba-badin shafi na : 429.
*Amsawa✍????*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
4\2\2015