Jamb

Cikakken Tarihin hukumar Jamb

Wannan hukuma cibiyace ta shirya jarabawar Shiga Jami’a tare da sauran cibiyoyi na ilimi a Nigeria kamar irinsu Polytechnics da Colleges, kuma mutum zaisamu damar yin jarabawar ne matukar dai ya kammala karatunsa na sakandare.

> Wace hanya akebi a shiga Jami’ a kirkiri hukumar jamb ?

Kafin akirkiri wannan hukuma ta jamb, Nigeria tanada jami,o,i ne guda shida zuwa bakwai a shekarar 1974 kenan. Kowace jami,a daga cikinsu tana shirya jarabawarta ne kuma tadauki adadin daliban da sukayi Nasarar cin jarabawar. Ana cikin hakan karkashin jagorancin mulkin Chief Olusegun Obasanjo a shekarar ya kara kirkirar wasu jami,o,i guda shida (6), bayan haka kuma sai gwamnatin ta kafa wani kwamiti dazai rika kula da jarabawar ta shiga jami,a karkashin shugabancin Mr. M. S Angulu.


Bayan haka sai wannan kwamitin ya bada shawarar akafa wasu hukumomi guda biyu, wato; CENTRAL ADMISSION BOARD da kuma JOINT MATRICULATION BOARD. Gwamnatin mulkin soja na wannan lokacin ta amshi shawarorinda kwamitin ya bata inda ta kirkiri JOINT ADMISSIONS AND MATRICULATION BOARD, daga nan sai aka kafa hukumar a shekarar 1978, 13th February, A karkashin dokar kundin tsarin mulkin soja ta Nigeria shekarar 1978. (Decree No. 2 of the federal military government of Nigeria)


Hakanan a shekarar 1988 watan August akayi gyara a kundin tsarin mulkin sojan na Nigeria No. 2 decree, Inda aka basu iko da damar shirya jarabawar domin shiga makarantun Polytechnics da Colleges of Education a duk fadin Nigeria.
Sannan wannan gyaran (Amendments) tun lokacin aka tsarashi aka rubutashi cikin kundin tsarin mulki na soja (Decree No. 33 of 1989, Of the federal military government).


Sannan ada anayin jarabawar ta jamb ne da takarda da pencil inda ashekarar 2012 Registrar na jamb awannan lokacin (Prof. Dibu Ojerinde) ya bada sanarwar cewa yanzu jarabawar zata kasance ne ta dayan hanyoyi uku;

1• Pepar and Pencil Testing (PPT)
Inda za,ayi jarabawar da takarda da pencil

2• Dibu Based Test (DBT)
Inda za,a kawo tambayoyin a kwamputa amma sai a amsa su a takarda

3• Computer Based Test (CBT)
Shikuma anan da tambayoyin da kuma amsasu duka zai kasancene a cikin komputa din.

Hakan ya farune sakamakon wasu da dama daga cikin dalibai suna rasa sakamakon jarabawar tasu saboda bacewar takaradar da suka amsa jarabawar.

See also  Bayani Gameda Two Sittings Tareda Yadda Ake Amfani Dashi


Hakazalika wannan jarabawa anayinta ne sau daya ashekara inda akowace shekara ake samun kimanin dalibai miliyan daya da suke zaunawa jarabawar. Amma awannan shekara da muke bankwana da ita (2017) an samu kimanin dalibai Miliyan daya da dubu dari bakwai da suka zauna jarabawar (1.7 Million) Kuma jarabawar tanada darasi hudu ne;

English Language:


Wanda dolene sai kowanne dalibi yayishi, saikuma sauran darasi uku dasukeda alaka da kwas (Course) dinda kakeso kakaranta a jami,ar, sannan jarabawar tana dauke da tambayoyi guda dari biyu da hamsin (250) inda English yakeda tambaya 100, sauran darusa ukun kuma sunada hamsin hamsin (50) amma awannan shekarar (2017) da muke bankwana da ita anrage yawan tambayoyin inda aka dawo dasu 180 gaba dayan darusa hudun, English aka bashi tambaya 60, sauran darusan kuma aka basu tambaya 40 sannan kuma jarabawar a shekarun baya tanada lokacine dayakai tsawon awa uku da minti goma, (3 hours, 10 minutes) amma shima anrage inda aka mayardashi awa biyu kacal, (2 hours) Sannan adadin maki din jarabawar yananan yadda yake bai canja ba wato (400 Marks).

Sannan maki mafi karanci da akeso dalibi ya samu shine 180, inda a Shekarar 2007 maki din yake 160, a shekarar 2008 kuma aka karashi yazama 170, sannan a shekarar 2009 aka mayardashi 180, a shekarar 2017 kuma abun mamaki sai hukumar ta rage yawan maki din daga 180 ta dawo dashi 120, Wanda yin Hakan yasha suka daga bakin al’ummar Nigeria Wanda akarshe hukumomin Jami,o,i suka dinga Kara Maki din daga 120 zuwa yanda Suke ganin yayi Musu Dai Dai.

See also  Tambayoyi (40) da suke yawan fitowa Biology a Jarrabawar JAMB tare da amsa


a Shekarar 2018 Kuma Hukumar Jamb ta Mayar da cut off marks din Zuwa 140,Yayinda a Shekarar 2019 Kuma ta Mayar dashi 160.


So duk da haka yakamata musani kowace university tanada adadin maki dinda takeso, ya danganta ne da irin kwas dinda kakeso kakaranta. Ba lallai ne Dan kaci 160 dinba kasamu admission.

To ko Yaya zanyi in shiga jami,a ta hanyar jamb ?



Wannan abune mai sauki, kawai abinda zakayi shine kaje ka bude profile a shafin yanar gizo na jamb din www.jamb.gov.ng daganan saikaje banki kabiya kudin Da’aka tanada na Shekarar Nan Wanda Har yanzu basu fidda ba.


sukuma bankin zasu baka wata lamba da akecema e-pin to idan suka baka saikaje daya daga cikin ofishin hukumar ta jamb dan yimaka rajista kokuma kaje daya daga cikin centers din da hukumar ta basu lasisin yin jarabawar. Idan zakatafi saikaje da O’ level dinka (Waec/Neco/Nbais/Nabteb) sannan katabbata kaci darasin English da ilimin lissafi (Mathematics) kuma katabbata kaci darasinda yakeda alaka da kwas dinda kakeso kakaranta a jami,ar.

Sannan idan lokacin jarabawar yayi zasu sanar daku, kuma katabbata kaci maki dinda baigaza 160 Ba, (amma fa wannan na shekarar da Mike bankwana da itane 2019, yanzu bamusan yaya abun zai kasance ba a 2020) domin shine maki mafi karanci a jamb din (minimum).

To idan Kayi nasarar cin jarabawar wannan shine zai baka damar da zakaje kayi Jarabwar Post-UTME (POST-JAMB) A jami,ar da kake neman admission din. Idan akayi shima kaci to jami,ar da kanema zata baka admission inda zaka fara daga aji daya, (Level 100 /Level 1 / UG 1) to shikenan ka shiga jami,a. Sannan zaka shekara hudu idan kwas din mai shekara hudu ne, ko kumashekaru biyar idan Mai shekaru biyar ne.



Miftahu Ahmad Panda

See also  Yadda ake karanta Past Questions

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button