Madannai 9 da zaka iya amfani dasu a madadin Mouse lokacin Jarrabawar Jamb
Tun bayan mayar da jarrabawar Jamb a Na’ura Mai kwakwalwa, Hakika Dalibai da dama kan fuskanci Kalubale a lokacin gudanar da jarrabawarsu ta Jamb, sakamakon karancin Ilimin Na’ura mai kwakwalwa,wasu Dalibanma kan Gaza gudanar da jarrabawar tasu sakamakon wannan matsala, Hakanne yasa Hukumar ta Jamb ta baiwa Dalibai damar yin amfani da wasu madannai Guda 9 a madadin yin amfani da mouse, saboda wasu daga cikin Daliban kan kasa yin amfani dashi.
Madannan Guda 9 Sune;
1. A- zaka Iya danna Mabullin A a cikin Keyboard dinka, idan kanason ka zabi amsar A, basai ka jawo Cursor dinka ka kaishi kan A dinba, kawai da zarar ka danna A, zai zabar maka amsar A
2. B – Idan amsar ka B ce, kawai sai kadanna Madannin B, batare da kayi amfani da mouse ba
3. C – idan kuwa amsar ka C ce to sai kadanna Mabullin C kawai, domin zabar C
4. D – Idan kuwa yakasance D ne amsarka to sai kadanna D a cikin Keyboard dinka, zai zabar maka zabi na Hudu wato D
5. P – Idan kuwa so kake ka koma tambaya ta baya, kawai ka danna Mabullin P zai kaika tambayar baya, ma’ana tambayar da ka wuce
6. N – Idan kuwa so kake ka tafi tambaya ta Gaba, Abin da zakayi kawai shine Danna Mabullin N zaka tsinci kanka a tambaya ta Gaba
7. S – Bayan ka kammala jarrabawarka, Idan kanason kayi submitting, ma’ana ka turawa Hukumar Jamb Jarrabawar ka, kawai sai kadanna Mabullin S
8. R – Idan kuwa da danna Mabullin S a bisa Kuskure, to abin da zakayi shine Danna mabullin R domin mayar dakai inda zakaci gaba da gudanar da jarrabawarka
9. Y – Idan kuwa ba abisa kuskure kadanna Mabullin S dinba, ma’ana idan so kake kayi submitting din Jarrabawar taka, to da akwai bukatar kadanna Mabullin Y bayan kadanna Mabullin S din, domin kuwa Jarrabawar taka bazatayi Submitting ba koda kadanna Mabullin S, matukar baka danna Mabullin Y ba.
Wadannan madannai da muka lissafo, sune madannai 9 da Hukumar Jamb ta baiwa Dalibai damar yin amfani dasu a madadin Mouse.
Yanada kyau kayi Sauri sosai a lokacin da kake gudanar da Jarrabawar ka ta Jamb, domin kuwa Ana bukatar ka amsa dukkanin tambayoyin da za’ayi maka guda 180, a cikin mintuna 120 (Awa Biyu)
Kada kawuce Second 40 a kowacce tambaya, saboda baka da lokacin Bata Lokaci.
Mungode
Marubuci: Miftahu Ahmad Panda