ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI’A NE ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Mal. Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci.
Ina matsayin haka a sharia?
Amsa:
To dan’uwa jan carbi ba bidi’a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi (s.a.w) hakan ba zai sa ya zama bidi’a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.
Yin amfani da ‘yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za’a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.
Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.
Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi (s.a.w) yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu- dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, sai dai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi.
Sai dai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi’a, ga shi kuma ba’a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.
Don neman Karin bayani duba : Majmu’ul fataawa 22\187. da Lika’ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Zarewa
24\3\2015