Halayen Annabi Muhammad (SAW)Nasiha

Kulawar Annabi Ga Masu Bukata Ta Musamman (Nakasassu)

A wata rana Manzon Allah (saw) ya gana da fitattun shugabannin Quraishawa Utbah bn Rabiah da dan uwansa Shaybah, Amr bn Hisham wanda aka fi sani da Abu Jahl, da Umayyah bn Khalaf da Walid bn Mughirah. Ya fara magana da tattaunawa da su yana ba su labarin Musulunci. Sosai ya yi fatan su amsa masa da kyakykyawan sakamako kuma su musulunta, ko kuma su janye gallazawar da suke yi wa sahabbansa.

Ana cikin haka sai Abdullahi bn Umm Maktum, Wani makaho sahabin Manzon Allah (saww) kullum yana sha’awar haddar Alqur’ani, ya zo ya tambaye shi ya karanta wata aya daga cikin Alqur’ani. Ya ce: “Ya Manzon Allah, ka karantar da ni daga abin da Allah Ya sanar da kai.”

Sai Annabi ya daure fuska ya kau da kai daga gare shi. A maimakon haka sai ya karkata akalarsa zuwa ga Shugabanin Kuraishawa, yana fatan za su zama musulmi, kuma da yarda da Musulunci za su daukaka addinin Allah da karfafa aikin sa. Da ya gama yi musu magana ya fice daga taronsu, A nan ne ayoyi goma sha shida na farkon suratu Abasa suka sauka, suna tsawatar wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan Abdullahi dan Umm Maktum, ayoyi goma sha shida wadanda ake ci gaba da karanta su tun daga wancan lokaci har zuwa yau, kuma za a ci gaba da karanta su har Abada.

Tun daga wannan rana Annabi bai gushe yana yi wa Abdullahi bn Ummu Maktum kyauta ba. Yakan tambaye shi al’amuransa, don biyan bukatunsa da shigar da shi cikin majalisarsa a duk lokacin da ya zo. Hasali ma, ya yawaita gai da Ibn Umm Maktum da wadannan kalmomi na tawali’u: “Maraba zuwa gare shi wanda Ubangijina ya tsawatar da ni”.

See also  MU AMBACI ALLAH AMBATO MAI GIRMA

Halin Annabi ga nakasassu misali ne mai kyau a gare mu. Bayan gaisawa da Abdullahi bn Ummu Maktum cikin girmamawa da kaskantar da kai, Annabi ya Sha nada shi a matsayin shugaban Madina sau da Dama, Makantar Abdullahi bn Ummu Maktum ba ta hana shi gudanar da ayyukansa ba.

Duk da cewa Annabi ya kasance mai kula da halin da sahabbansa nakasassu bai daukarsu a matsayin Wulakantattu ya Daukarsu Kamar Yadda Yake Daukar Sauran Sahabbansa.

Don haka, mu ajiye son zuciya da zato, dole ne mu gane cewa nakasa a kanta ba Ba mutum ne ya janyowa kansa cikas ko lahani ba. Wannan shine ƙarin dalilin da ya sa ya kamata mu ƙara ƙoƙari don samar da sauƙi ga nakasassu ta hanyar tabbatar da jin daɗinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button