Tambayoyi a Musulunci

MAGANIN QARFIN MAZA



Tambaya
Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. Jameel imani da lafiya da ilimi, gaskiya muna amfana

Amsa:
Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma’aurata turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin ka’idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum wadanda ba ibada ba ne sun halatta, in har ba’a samu nassin da ya hana ba.

Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
23/05/2016

See also  SHIN ALLAH YANA YIN ABUBUWA DA HIKIMA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button