AMFANI DA MOTAR OFFICE A HARKOKIN KASHIN-KAI
Tambaya:
Assalama alaikum Malam ya halatta mutum ya zuba mai a motar ma’aikatar da yake aiki, ya kai matarsa unguwa, ko ya je harkokinsa na yau da kullum, a ciki ?
Amsa:
Wa alaikum assalam To dan’uwa kwamitin fatawa na din-din na Saudiyya ya bada fatawa cewa: Bai halatta mutum ya yi amfani da motar gwamnati wajan harkokinsa na yau da kullum ba, tun da ba dan haka aka tanaje ta ba, kamar yadda ya zo a fatawa mai lamba ta: 16594.
Sheik Ibnu Uthaimin yana cewa: “Ko da shugabanka na office ya halatta maka, bai halatta ba, tun da b a huruminsa ba ne, ba kuma mallakinsa ba ne, kamar yadda ya zo a: Lika’u babil maftuh: 238.
Yana daga cikin siffofin muminai kiyaye amanar da aka damka a hannunsu, kamar yadda aya ta: 8 a suratul Muminuna ta tabbatar da hakan.
An rawaito cewa Khalifa Umar dan Abdul’aziz ba ya amfani da fitilar gwamnati a harkokinsa na kashin-kai, ko da kuwa bako ya yi bai zai yi hira da shi da fitilar gwamnati ba, in har ba matsalolin da suka shafi jama’a za su tattauna ba, wannan sai ya nuna taka-tsantsan da dukiyar office yana daga cikin tsentseni.
Duk dukiyar Gwamnati ta Jama’a ce, wannan yasa ba a amfani da ita sai a harkokinsu na yau da kullum.
Duk wanda ya wadatu Allah zai wadatar da shi, wanda ya kame Allah zai kamar da shi, Wadatar zuci taska ce da ba ta karewa.
Allah ne mafi Sani.
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
25\2\2016