Addu'o'i

Karanta Addu’ar Tsayuwa a Kan Dutsen Safa da Na MarwaJabir, Allah ya yarda da shi ya ce, yayin da yake siffanta hajjin Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; yayin da ya kusanto dutsen Safa sai ya karanta:
إِنَّ الصَّفَا وَالْمَرْوَةَ مِنْ شَعَائِرِ اللهِ.
أَبْدَأُ بِمَا بَدَأَ اللهُ بِهِ.
Bers Safa: Innas safa wal marwata min sha’a’irillah
Abda’u bima bada’al lahu bihi.

Hakika Dutdsen Safa da na Marwa suna daga cikin alamomin da Allah Ya sanya (na addininsa)”.

Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi.

Sannan ya fara da Dutsen Safa, ya hau shi har sai da ya hango dakin Allah, sai ya fuskanci alkibla, ya kadaita Allah, (ya yi hailala), ya girmama shi (ya yi kabbara) ya ce;
اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ! اللهُ أَكْبرُ!
Allahu akbar. Allahu akbar. Allahu akbar.
Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma.

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ، اَللهُ أَكْبَرْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ أَنْجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عَبْدُهُ، وَهَزَمَ اْلأَحْزَابُ وَحْدَهُ.
Bers la Ka’aba: La ilha illallahu, allahu akbar, La ilaha illal lahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wa huwa ala kulli shay’in kadirun. La ilaha illal lahu wahdahu. Anjaza wa’adahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzaba wahdahu.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki ya tabbata a gare shi, kuma yabo ya tabbata a gare Shi; kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai. Allah ya gaskata alkawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai Shi kadai.

Ya karanta wannan zikiri sau uku, yana yin addu’a bayan kowace marra. Da ya hau Dutsen Marwa ma ya yi kamar yadda ya yi a kan Dutsen Safa.

See also  Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button