YADDA ZAKU YI CONVERTING HARD COPY NA DOCUMENT ZUWA SOFT COPY CIKIN SAUƙI DA WAYARKU TA HANNU
Yana da muhimmanci sosai ku iya wannan converting din, musamman ma ‘dalibai domin akwai buƙatar hakan sosai ko wajen assignment ko project ko wani abun daban idan an samu data wadda take a hard copy, sannan yan’uwa masu yawan yin research da rubuce-rubuce suma suna buƙatar wannan, haka zalika masu sana’ar printing ma suna buƙatar shi matuƙa, kasantuwar ana kawo hard copy na document ace ana son ayi editing nashi, kunga cikin sauƙi za suyi shi in sha Allah.
Da farko dai zaka samu ka dauki hoton papers dinda rubutun da zaka mayar soft copy suke a jiki, sai ka samu kayi downloading na app din google translator da WPS document wanda zaka yi paste na rubutun da za ka dunga copying.
Ga yadda abun yake a mataki-mataki….
1- Idan ka bude app dinka na google translator zai baka za6uka harda wajen camera, sai ka danna wajen camera din.
2- Nanma zai baka za6uka harda wajen import, sai ka danna wajen import din.
3- Anan kuma za kaga hotunan dake cikin wayarka sun fito, sai kaje kan hoton paper ta document dinda ka dauka hoto sai ka danna.
4- Daga nan za kaga hoton yayi importing sannan zai fara scanning, yana gama scanning zai baka za6in clear da select all, anan kuma sai ka danna select all.
5- A wannan matakin na 5 kuma za kaga ya maka translating na rubutun zuwa yadda ka saka setting na app din, amma tunda babu ruwanka da translation din sai ka danna wajen translation din inda ya saka maka kibiya, za kaga ya wuce gaba ya fassara maka rubutun da yayi scanning din duka, daga nan idan kayi scrolling zuwa sama duka zaka ga rubutun da kayi scanning din original wanda ba’a fassara ba.
6- Daga nan sai kayi mark all na rubutun sai kayi copy, shike nan sai ka tafi cikin WPS dinka kayi paste, a haka zaka yi ma ko wace paper daka dauka hoto, abun yana da sauri idan an maida hankali kuma yana da sauƙi sosai.
Allah ya taimaka.
© Abu Ibrahim