Tech

Yadda Zaka Gano Wayar ka Ta Amfani Da IP-Address Dinta

Lokacin da nayi posting akan yadda zaka gano wayarka ta amfani da Gmail da number waya, da IMIE din waya amma sai naga kamar wasu haryanzu basu gane hanyar sosai ba, hakan yasa na nemo wata sabuwar hanyar mai kyau.

Wato irin wannan fasahar tuntuni kasashen turawa suke amfani da ita, amma kaga mu anan haryanzu bamu ma santa ba, saboda bamu dauki harkar Technology da wani muhimmanci ba, shiyasa kullun muke a baya ta bangaren Technology.

Ita wannan Fasaha zata baka damar bibiyar wurin da wayarka take koda kuwa anyi formatting wayar, ko ancire Gmail dinta ko IMIE dinta, saboda kunsan yanzu suma masu satar wayar Allah ya basu hikimar cire Imie din waya da Gmail din da sauransu ta yadda baka isa kabi diddigin su ba, to amma kunga idan mukayi masu amfani da IP-Address din wayar ai lokaci daya sai ku kamasu in sha Allah..

Farko nasan ba kowa yasan IP-Address din wayarsa ba, dan haka yanzu inaso kowa yaje setting din wayarsa, kana shiga setting sai kaje wurin da aka rubuta “About Phone” sai kashiga kana shiga zakaga wurin da aka Rubuta “Status” sai kashiga anan zakaga IP din wayarka, idan kuma baka gane ba, sai kaje Google kawai ka nemi yadda zakasan IP dinka.

Bayan kaga IP din wayar naka sai kasamu takarda da biro ka rubuta abunka domin zai maka amfani sosai koda hakan ta kasance.

To yanzu mu qaddara an dauke maka wayar naka to amma daman kariga da ka dauki IP-Address din wayar ka adana shi a kasan akwaitinka..

See also  Maganin Barayin Waya, Da Masu Cire Maka Caji Su Saka Tasu Wayar Baka Sani Ba

To Abinda zakayi anan shine; zaka dauko wannan IP din naka kaje browser din computer dinka, zaka iya amfani da wayar Abokinka amma da Computer yafi nuna maka komai yadda yakamata, to koma dai menene idan kabude browser dinka sai kashiga wurin search Engine din sai ka rubuta “IP Locator” kana rubuta wa zai bude maka zai nuno maka abubuwa da yawa akan “IP Locator” to kai sai ka dauki na farkon wanda zakaga an rubuta; “IP Locator Finder – Geolocation” sai kawai kayi ka taba shi, kashiga cikinsa kai tsaye, yana budewa zakaga yanayin yadda cikinsa yake, da rubuce rubuce haka dai, to sai ka natsu zakaga wurin da aka rubuta; “IP Locator” da alamar dan akwatin bincike a kasan rubutun, to acikin wannan dan akwaitin binciken sai ka rubuta wannan “IP” din naka wanda ka rubuta kafin wayarka ta bata, sai ka rubuta shi aciki, daga gefen akwaitin zakaga wani rubutu an rubuta; “IP Lookup” kawai sai ka danna shi kai tsaye, bayan ka danna zakaga yafara searching bayani ya gama zai bayyanar maka da wasu rubutu haka acikin table, da sunan kasar da IP din yake to kaikuma sai ka natsu zakaga wurin da aka rubuta; “Latitude” da “Longitude” to kana ganinsu sai kayi Minimizing kaje Google browser sai kayi searching Google Map (shiyasa nace da Computer aikin zaifi sauqi saboda sai dai kawai kayi “New Tab”)

To Google map dinka yana budewa, sai ka koma wajen ” Latitude ” dinka kayi copy dinsa sai ka koma Google map dinka sai kaje wurin da akeyin searching sai kayi pasting din “Latitude numbers” din a wurin kana ajiye su a wurin sai ka danna space a tsakaninsu (ka tabbatar kabada space) daganan sai kaje kayi copy din “Longitude” sai kazo ka ajiye shi a kusa da “Latitude” dinka shiyasa nace ka tabbatar kabada Space tsakaninsu, kabada space tsakanin “Latitude Numbers din da Longitude numbers” kana ajiyesu kawai sai ka danna Searching.
Kana danna searching zaifara searching,  yana gamawa zai bayyanar wurin da IP din yake (Zakaga alamar Locator wadda zakaganta Ja (Red)) to kai kuma sai dinga Zoming wannan Alamar domin gano daidai unguwar da yake.

See also  Matakan Da Zakabi Idan Kanason ƙirƙirar Shafin Yanar Gizo (Website)

Sannan kunsan shi Google map yadda yake, zata iya yiwuwa kana zoming din amma baka sameshi ba, to kawai sai kaduba daga hagunka, zakaga inda aka rubuta “Setilayit” da alamarsa, sai ka danna wurin kai tsaye, kana dannawa zai bayyanar maka harda gidajen unguwan da wayar naka take, da sunayen unguwannin da sauransu. Shikenan ka gama.

Amma a kasashen waje da sukeda cigaba a cikin Google map din naka zakaga wata alamar dan yaro haka, zaka daukota ka ajiyeta daidai wurin wannan “Locator” din ja (red) to zaiyi searching kadan daganan kawai sai kaga ya kawo ka har gidan da wayar taka take da wurin da take da sauransu..

Allah yataimaka 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button