Tech

Yadda Zaka Ɓoye Number Ka Yayin Tura Saƙo (Text Message)

Wasu ƙasashe da suka cigaba Al’ummar ƙasar nasu sukan tura saƙo tsakaninsu batareda number wanda ya tura saƙon ya bayyana ba saboda layukan sadarwan ƙasar nasu ya basu damar yin hakan, Amma mu a nan Nigeria gaskiya babu wani kamfanin Layi da ya bada damar hakan, kuma bawai dan bazai yiwu ba sai dai dan kawai basu yarda da hakan ba amma mu kuma yan Technology akwai wasu dabaru da mukeyi wanda muma zamu tura saƙon Message batareda number namu ta bayyana ba.

Yadda abun yake shine idan ka shiga ”Message” na wayarka sai ka nemi “Message Setting” wato ɓangaren Setting na message ɗinka, a ciki zakaga wurin “Text message” sai kashiga idan ka lura zakaga “SMS Sending Profile” sai ka danna wurin ”Option” zakaga sun rubuta maka “SEND SMS AS” wurin da aka rubuta ”Send SMS AS” sai ka zaɓi zuwa ”Email’. Idan ka zaɓi ”Sending SMS” ta ”Email” sai ka danna zai tambayeka kasa ”SMS Server” sai kasa lambar layinka wanda kake son ka ɓoye yayin da kake son tura saƙon, sai ka danna ”Save” sannan ka danna ”Activate”.

Nan take bayan kagama sai ka koma wurin rubuta saƙo sai ka rubuta saƙon da kakeson turawa, bayan ka gama sai ka danna ”Send”, zasu tambayeka ka rubuta “Email Address” sai ka rubuta abinda kake so as “Email” Misali: Saheel@gmail.com ko kuma wani suna da kake buƙata.

Idan ka gama sai ka danna ”Send” nan take saƙon Message ɗin zaije wurin wanda ka tura mawa da cewar daga Saheel@gmail.com, saɓanin lambar wayarka.

See also  Best 5 Steps To Improve Your Programming Skills

Ida kanada kamfani kana iya amfani da wannan hanyar wurin tura saƙonni ga ma’aikantaka ko makamancin hakan..

Allah Yataimaka..????

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button